Gwamnatin Tinubu Ta Fito da Hanyar da Jihohi za Su Magance Matsalar Lantarki

Gwamnatin Tinubu Ta Fito da Hanyar da Jihohi za Su Magance Matsalar Lantarki

  • Gwamnatin tarayya ta bukaci jihohin Najeriya su karɓi ragamar samar da wutar lantarki da raba ta ga al'ummarsu
  • Ministan makamashi na kasa, Adebayo Adelabu, ya ce hakan ne kawai mafita ga matsalar wutar lantarki a kasar
  • Ya ce jihohi 15 sun riga sun samu ikon kansu na gudanar da harkar lantarki bisa dokar wutar lantarkin Najeriya ta 2023

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Gwamnatin tarayya ta bukaci jihohi 36 na Najeriya da su kafa kamfanonin samar da wutar lantarki domin magance matsalar rashin wuta da ta dade tana damun kasar.

Ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a Legas, inda ya ce tsarin da ake da shi yanzu bai dace da girman Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Cigaba: Najeriya ta fara fitar da kayan sola da ta kera zuwa ketare

Bayo Adelabu
Ministan makamashi, Bayo Adelabu. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Twitter

Punch ta rahoto ya ce dokar wutar lantarki ta 2023 da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta rattaba hannu a kanta ta ba jihohi damar gudanar da harkokin samar da wuta da kansu.

Minista ya fadi matsalar wuta a Najeriya

Adelabu ya ce Najeriya kasa ce mai fadin gaske da yawan jama’a da harkokin kasuwanci masu tarin yawa, don haka ba za a iya tafiyar da wutar lantarki daga Abuja kadai ba.

“Ba za ka iya daga Abuja ka tabbatar da wuta mai dorewa ga dukkan jihohi ba. Wannan dalili ne yasa muka bude kofa wa jihohi su shiga cikin harkar samar da wuta,”

- Inji shi

Ya ce gwamnatin tarayya tana aiwatar da shirin gyaran bangaren wuta ta hanyar inganta dokoki, samar da manufofi, gina sababbin kayayyakin aiki, da kuma karfafa saka hannun jari.

Adelabu ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya daukar nauyin dukkan kudin da ake bukata a bangaren lantarki ba saboda akwai sauran sassa masu bukatar kudi kamar ilimi, lafiya, tsaro.

Kara karanta wannan

An dauke wutar lantarki a arewa yayin da mahara suka lalata kayayyakin TCN

Jihohi 15 sun fara kafa hukumomin wuta

Ministan ya bayyana cewa tun bayan amincewa da dokar wutar lantarki ta 2023, jihohi 15 sun samu cikakken ikon kansu kan harkar lantarki, ciki har da jihar Enugu.

Wutar lantarki a Najeriya
Wasu layukan wutar lantarki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce gwamnati na aiki tare da wadannan jihohi domin tabbatar da daidaiton kasuwar rarraba wuta tsakanin jihohi da kasa baki daya.

“Hukumar samar da wuta a karkara (REA) ta riga ta gudanar da taruka da gwamnoni fiye da 20 don tattaunawa kan yadda za a bunkasa shirin samar da wuta a yankunan da ba su da ita,”

- Adebayo Adelabu

Adelabu ya nemi jihohi su tashi tsaye

Ministan ya bukaci gwamnoni da su dauki matakan da suka dace wajen amfani da ikon da suka samu kan samar da wutar lantarki.

“ Dole jihohi su nuna bajintarsu. Kada magana kawai ta tsaya a baki. Ya kamata su gayyaci masu zuba jari na cikin gida da na waje domin kafa masana’antun samar da wuta ta hanyoyi daban-daban — wutar gas, ruwa, sola, ko iska,”

Kara karanta wannan

An gano daloli, motoci da alfarma da Tinubu ya ware wa korarrun hafsoshin tsaro

- Inji Ministan

Ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsaron makamashi a jihohi, musamman ma saboda yawancin jihohi suna da girman da ya kai wasu kasashen Afirka.

Najeriya ta fara fitar da kayan sola waje

A wani labarin, mun rahoto muku cewa Najeriya ta fara fitar da kayan sola kasashen waje bayan kera su a cikin gida.

Ministan makamashi na kasa, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka yayin wani taro da aka gudanar a jihar Legas.

Ya bayyana cewa hakan na cikin yunkurin gwamnatin Tinubu na habaka makamashi a gida da ma nahiyar Afrika baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng