Sanusi II Ya Yi Korafi kan Yawan Kashe Kudi da Gwamnatin Tinubu ke Yi

Sanusi II Ya Yi Korafi kan Yawan Kashe Kudi da Gwamnatin Tinubu ke Yi

  • Muhammadu Sanusi II da Atedo Peterside sun ce gyare-gyaren gwamnati ba za su amfanar da ‘yan kasa ba sai an rage kashe kudi
  • Sun yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan cire tallafin man fetur amma suka soki yadda ake kashe karin kudin da aka samu
  • A bayanin da suka yi a wani taron kan tattalin arziki a Abuja, sun bukaci shugabanni su rungumi gaskiya da rikon amana a tafiyar da mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, tare da fitaccen masani kan tattalin arziki, Atedo Peterside, sun yi kira ga gwamnatin tarayya kan rage yawan kashe kudi.

Sun bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arziki da Bola Tinubu ya ce ya yi kadai ba za su wadatar da kasa ba.

Kara karanta wannan

"Ku daina": Sanusi II ya gano kuskuren da ministoci da hadimai suke yi ga shugaban kasa

Sarki Muhammadu Sanusi II
Mai martaba Sanusi II yana hira da manema labarai. Hoto: Masarautar Kano
Source: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa sun bayyana haka ne a taron Oxford Global Think Tank da aka gudanar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II: “Me ya sa ake da ministoci 48?”

Sanusi II, wanda tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ne, ya bayyana cewa yawancin matsalolin tattalin arzikin kasar suna faruwa ne saboda rashin bin shawarar masana.

Ya ce dole ne gwamnati ta fahimci tsarin tattalin arziki da yadda manufofi ke aiki, yana mai cewa:

“Rashin sanin yadda tattalin arziki ke aiki yana haifar da yanke shawara maras kyau.”

Sanusi II ya tuna yadda gwamnatin Jonathan ta yi yunkurin cire tallafi a 2012 amma aka hana, inda ya ce Babban Bankin Najeriya a lokacin ya dauki matakai don guje wa hauhawar farashi.

Ya ce:

“Matsalar mu ita ce rashin taka tsan-tsan da yawan kashe kudin gwamnati. Me ya sa ake bukatar ministoci 48 masu jerin motoci?”
Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana sanya hannu a wata takarda. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sanusi II ya ce a fadawa gwamnati gaskiya

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya kare manoma daga asara yayin da farashin abinci ya sauka

Punch ta wallafa cewa Sanusi II ya ce yawancin shugabanni ba sa sauraron shawarwarin gaskiya saboda suna son jin abin da zai faranta musu rai.

“Ana kallon mutanen da ke fadin gaskiya a matsayin makiyan kasa, yayin da masu yabon gwamnati ke samun tagomashi. Amma gaskiya ce kadai za ta ceci kasar.”

Ya bukaci shugabanni su zagaye kansu da mutanen da ke da gaskiya da mutunci, ba masu yaba musu ba, yana mai cewa hakan ne ke bata martabar ofisoshin gwamnati.

Maganar Peterside kan tallafin man fetur

Shi ma Dr. Atedo Peterside ya yaba da cire tallafin man fetur, amma ya ce ana bukatar tsari da gaskiya wajen amfani da karin kudin da ake samu.

Ya ce:

“Na dade ina goyon bayan cire tallafi tun shekaru 30 da suka gabata, amma dole mu yi tambaya: me ake yi da kudin da ake samu daga hakan?”

Jawabin Edun a taron su Sanusi II

A wani bangare kuma, mun kawo muku bayanin da ministan kudin Najeriya, Wale Edun ya yi a taron da mai martaba Sanusi II ya jagoranta kan tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Wale Edun ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na daukar matakai domin rage radadin wasu gyare-gyare da ya yi.

Ministan ya kara da cewa a yanzu haka za a fadada shirin raba tallafin kudi kai tsaye ga miliyoyin 'yan Najeriya a dukkan kananan hukumomi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng