DSS Ta Cafke Mutumin dake Kokarin Tunzura Sojoji Su Kifar da gwamnatin Tinubu

DSS Ta Cafke Mutumin dake Kokarin Tunzura Sojoji Su Kifar da gwamnatin Tinubu

  • Jami'an hukumar tsaro ta DSS ta kama wani matashi da ake zargi da kiran juyin mulki a kafar sada zumunta
  • An gano wanda ake zargi a Oyigbo, jihar Ribas, bayan ya wallafa sakonnin tada zaune-tsaye kan shafinsa na sada zumunta
  • Rahotanni sun ce jami'an DSS na ci gaba da bincike kuma wanda ake zargin yana ba da hadin kai yayin da aka rufe shafinsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers –Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wani mutum mai suna Innocent Chukwuma a yankin Oyigbo, da ke jihar Ribas, bisa zargin yin kira ga sojoji su kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Wannan kame na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da rade-radin cewa wasu sojoji sun shirya juyin mulki a cikin watan Oktoba, 2025 kafin a dakile yunkurin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama Darakta janar da ake zargi da hannu a 'shirin juyin mulki'

Jami'an DSS sun kama matashin dake kira a yi juyin mulki
Alamar hukumar DSS da Bola Ahmed Tinubu Hoto: @ZagazOlaMakama/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa shafinsa na X cewa Innocent Chukwuma ya yi amfani da shafinsa na X mai suna @TheAgroman, wajen tunzura sojojin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi ya nemi a yi wa Tinubu juyin mulki

Rahoton ya kara da cewa Innocent Chukwuma ya wallafa sakonni da ke kiran sojoji su karbe mulki tare da dakatar da gwamnatin da ke shugabanci a yanzu haka.

A cikin daya daga cikin sakonninsa, Chukwuma ya rubuta cewa:

“A Najeriya muna bukatar juyin mulki. A kori APC, a dakatar da gwamnati, a hada kai da AES — wannan ne kawai mafita yanzu. Wata rana hakan zai faru. Sojoji ne kadai za su iya ceto wannan kasa.”

Ya kuma zargi gwamnati da sayar da kasar ga kasashen yamma, yana mai cewa:

“Wanda ke Aso Rock ya sayar da Najeriya. Yammacin duniya ke tafiyar da harkokin leken asiri. Sojoji ne kadai za su iya saita kasar nan daga farko.”

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Yan bindiga sama da 80 sun bakunci lahira da suka yi yunkurin shiga Kebbi

DSS na binciken mai kiran juyin mulki

Majiyar tsaro ta bayyana cewa an kama Chukwuma ne bayan an bi diddigin sakonninsa a dandalin sada zumunta, sannan aka gano inda yake a Oyigbo, jihar Ribas.

Wani jami’in DSS ya tabbatar da cewa wanda ake zargin yana hannun hukuma, kuma yana ba su hadin kai a yayin da ake ci gaba da bincike.

Yanzu haka DSS.na binciken Chukwuma
Taswirar jihar Ribas, inda aka kama Chukwuma Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tuni wasu matasan Najeriya suka fara bayyana ra'ayinsu a kan lamarin, inda suke ganin ya kamata a bibiyi yan ta'adda dake yawo a shafukan sada zumunta.

Wani @AkohKenneth ya ce:

“Me zai hana a kama ‘yan bindiga da ke wallafa bidiyo a TikTok ma?”

Har yanzu dai DSS ba ta fitar da cikakken bayani a kan batun ba, amma ana ci gaba da samun bayanai daga bakin Chukwuma.

Juyin mulki: Ana binciken tsohon gwamna

A baya, mun wallafa cewa wasu majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa an sanya ido sosai kan wani tsohon gwamna daga Kudancin Najeriya kan zargin hannu a batun juyin mulki.

Kara karanta wannan

Sanata Ned Nwoko ya fadi abubuwa 2 da za su dawo da zaman lafiya Kudu maso Gabas

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama hafsoshi 16 na rundunar soji da ake tuhumarsu da hulɗa a cikin wannan yunkuri na juyin mulki, duk da gwamnati ta ce babu wannan maganar.

Majiyar tsaro ta ce idan an tabbatar da alaƙa tsakanin tsohon gwamnan da waɗanda ake tuhuma, za a gayyace shi domin ya amsa tambayoyi game da shirinsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng