Darajar Naira Ta Karu a kan Dala, Ana Fatan 'Yan Najeriya Su Samu Sauki

Darajar Naira Ta Karu a kan Dala, Ana Fatan 'Yan Najeriya Su Samu Sauki

  • A ranar 28, Oktoba, 2025, Naira ta dan kara daraja a kasuwar musayar kudi ta NFEM yayin da kasuwar bayan fage ta ci gaba da zama daram
  • Farashin Dala a NFEM ya tsaya a kusan N1,457.06 kan kowace $1, yayin da na kasuwar bayan fage ke tsakanin N1,450 zuwa N1,480
  • Masana sun ce daidaiton na nuna tasirin matakan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dauka wajen rage bambanci tsakanin kasuwannin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, AbujaDarajar Naira ta dan karu idan aka kwatanta da Dala a kasuwar musayar kudi ta Najeriya (NFEM) a ranar Talata, 28 ga Oktoba, 2025.

Sai dai duk da haka, farashin ya cigaba da zama daram kamar yadda ya ke a kasuwar bayan fage ta canjin kudi.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ce an yi abin kunya a filin wasan Kebbi da aka gina da kudin FIFA

Dala Da Na
Hoton Nairar Najeriya da Dalar Amurka. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa ‘yan kasuwa da masana tattalin arziki na lura da yadda kasuwar ke wakana, musamman bayan wasu matakan da CBN ya dauka domin gyara tsarin musayar kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa darajar Naira a kasuwar NFEM ta dan tashi, lamarin da ke ba da fatan samun daidaito tsakanin kasuwannin kudi.

Farashin Naira da Dala a kasuwar NFEM

A rahoton yau, an bayyana cewa farashin Dala a kasuwar NFEM ya tsaya a kusan N1,457.06 kan kowace Dala daya ($1).

Wannan na nuna karuwar darajar Naira idan aka kwatanta da sa'o'i da suka gabata, inda Dala ke N1,458.

Masana sun bayyana cewa lamarin zai fi muhimmanci ga masu shigo da kaya, masu fitar da kaya, da kuma kamfanoni masu bukatar musayar kudi ta hanyar doka.

Farashin Dala zuwa Naira
Yadda farashin Dala ya ke zuwa Naira a yau. Hoto: Google Finance
Source: Facebook

Farashin Dala/Naira a kasuwar bayan fage

A kasuwar bayan fage, wadda ke biyan bukatun masu saye da sayarwa kai tsaye, an ce farashin ya tsaya ne ba tare da wani sauyi sosai ba.

Kara karanta wannan

Dangote ya taka sabon matakin arziki a duniya, ya mallaki Naira tiriliyan 43.8

Rahotanni daga dillalan kudi sun nuna cewa ana sayen Dala a tsakanin N1,450 zuwa N1,460, yayin da ake sayarwa a tsakanin N1,470 zuwa N1,480 kan kowace Dala daya.

Haka zalika, shafin Google Finance ya nuna cewa farashin Dalar Amurka 1 ya kai N1,458 a yau Talata, 27 ga Oktoban 2025.

Tasirin karuwar darajar Naira ga Najeriya

Masana sun bayyana cewa daidaituwar farashin Dala da Naira tsakanin kasuwannin biyu na nuna alamar ingantuwar tattalin arzikin kasa da karuwar gaskiya a harkar musayar kudi.

Ga masu shigo da kaya, an ce matakin na taimakawa wajen daidaita farashin kayayyaki, domin rage hauhawar kudin musaya.

A bangaren masu fitar da kaya kuwa, ana ganin hakan zai yi tasiri kan yadda za su samu riba idan suka sauya Dala zuwa Naira.

Ga matafiya kuma, daidaiton yana rage tazara tsakanin farashin kasuwa da na hukuma, wanda ke hana yin amfani da hanyoyin zamba wajen samun Dala.

IMF ya ce ana fitar da kudi daga Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa asusun ba da lamuni na duniya, IMF ya ce ana fitar da kudi daga Najeriya zuwa ketare ba bisa ka'ida ba.

IMF ya bayyana haka ne yayin taron shekara shekara da ya gudanar a kasar Amurka kuma ya yi kira a dauki mataki.

Kara karanta wannan

Majalisar Tarayya za ta shiga cikin lamarin karin kudin gidan haya

Gwamnan babban bankin Najeriya, Yemi Cardoso ne ya wakilci kasar saboda rashin lafiyar ministan kudi, Wale Edun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng