Gwamnan Kebbi Ya Yi Garambawul, Ya Sauyawa Wasu Kwamishinoni Ma'aikatu
- Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwar jihar wanda ya shafi wasu kwamishinonin da ke aiki a gwamnatinsa
- Nasir Idris ya sauyawa wasu daga cikin kwamishinoninsa ma'aikatun da suke aiki a wani mataki na kara bunkasa gudanar da ayyukan gwamnati
- A cewar sanarwar da sakataren gwamnatin jihar ya fitar, garambawul din da gwamnan ya yi zai fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya amince da yin wani dan karamin garambawul a gwamnatinsa.
Gwamna Nasir Idris ya amince da sauya wasu kwamishinoni biyu daga ma’aikatunsu zuwa wasu sababbin wuraren aiki, a cikin sauye-sauyen da ya yi a majalisar zartarwa ta jihar.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Yakubu Tafida, ya sanya wa hannu kuma ya rabawa manema labarai ranar Litinin, 27 ga watan Oktoban 2025 a Birnin Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa gwamnan Kebbi ya yi garambawul
A cewar Yakubu Tafida, sauyin wuraren aikin na daga cikin shirin gwamnan na sake fasalin ma’aikatun gwamnati domin tabbatar da ingantaccen gudanar da aiki yadda ya kamata ga jama’ar jihar, za a samu labarin a rahoton Premium Times.
Kwamishinonin da sauyin ya shafa sune, Samaila Yakubu Augie da Halliru Aliyu Wasagu.
An mayar da Samaila Yakubu Augie zuwa ma’aikatar lafiya, wacce ta zama babu kwamishina tun bayan dakatar da Yunusa Ismail bisa rashin yin aikinsa yadda ya kamata.
Haliru Aliyu Wasagu, wanda ya taɓa zama kwamishinan ma’aikatar ma’adanai, kafin a dakatar da shi kuma a maye gurbinsa da Garba Warah, yanzu kuma an mayar da shi zuwa ma’aikatar tsaro ta cikin gida.
“An umarce ni da na isar da amincewar Gwamna Nasir Idris na wannan sauyin wuraren aiki ga kwamishinonin da abin ya shafa."
"Wannan umarni an bada shi domin bin sa yadda ya kamata kuma zai fara aiki ne nan take."
- Yakubu Tafida
Yakubu Tafida ya yaba da haɗin kai da goyon bayan da sauran mambobin majalisar zartarwa ke ba gwamnati, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen cimma nasarorin da gwamnati ta samu zuwa yanzu.
Ya kuma jaddada cewa Gwamna Nasir Idris yana da kudirin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da ingantaccen hidimtawa jama’ar jihar Kebbi.

Source: Facebook
Karanta wasu labaran kan jihar Kebbi
- Gwamnati ta fito da 'barnar' Malami a Kebbi, ta faɗi yadda tawagarsa ta riƙa harbin iska
- An cafke dan jarida bayan fallasa gazawar gwamnatin Kebbi? An samu bayani
- Gwamnatin Kebbi ta tsage gaskiya kan batun 'yan bindiga sun kai kazamin hari a jihar
Gwamnan Kebbi ya dakatar da kwamishina
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya dakatar da daya daga cikin kwamiahinoninsa.
Gwamna Nasir Idris ya dakatar da kwamishinan lafiya, Yunusa Isma'ila bisa zarginsa da sakaci wajen gudanar da ayyukansa.
Hakazalika, gwamnan ya umarci kwamishinan da ya bayar da hujja mai karfi kan dalilin da zai hana daukar karin matakan ladabtarwa a kansa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

