Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno, an Tura Tsageru zuwa Barzahu
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama mai zafi da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno da ke fama da matsalar rashin tsaro
- Sojojin sun shiryawa 'yan ta'addan kwanton bauna, wanda hakan ya sanya suka hallaka su gaba daya
- Jami'an tsaron sun kuma kwato makamai masu tarin yawa daga wajen 'yan ta'addan wadanda ke kai hare-hare
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP guda 10 a jihar Borno.
Sojojin sun kuma kwato makamai da kayan aiki a samamen da suka kai da daddare a hanyar Gamboru–Dikwa–Marte da ke jihar Borno.

Source: Facebook
Jami’in yaɗa labarai na rundunar Joint Task Force (Arewa maso Gabas) Operation Hadin Kai, Laftanal Kanal Sani Uba, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka sanya a shafin X.
Sojoji sun kashe 'yan ISWAP a Borno
A cewar sanarwar, samamen ya biyo bayan wata fafatawa da sojoji suka yi da ‘yan ta’adda a yankin Katarko, inda aka kashe sama da ‘yan tsageru guda 50 a baya.
Laftanal Kanal Sani Uba ya ce sojojin sun kaddamar da samame cikin kwarewa, wanda ya hana ‘yan ta’adda shigowa daga yankin Flatari zuwa Gamboru Ngala.
Ya ce bayan da ‘yan ta’addan sun yi asara mai yawa, sun karkata zuwa yankin Dikwa, amma sojojin sun sake tarar da su a hanyar Dikwa–Marte inda suka kashe su gaba ɗaya.
“Da misalin karfe 11:50 na daren ranar 25 ga Oktoba, yayin da dakarun ke wurin da suka boye don kwanton bauna, sun hango mayakan tare da kai musu farmaki."
- Laftanal Kanal Sani Uba
Ya kara da cewa zuwa washegari, sojojin sun gudanar da aikin tsabtace yankin gaba ɗaya, inda suka tabbatar da kashe ‘yan ta’adda 10.
Sojoji sun kwato makamai
Abubuwan da aka kwato daga wurin sun haɗa da bindigogin AK-47 guda biyar, babbar bindigar PKT guda daga da sauran makamai.

Source: Original
Haka kuma an kwato manyan harsasai masu kaurin 7.62x54mm, babura guda biyu, keken hawa guda, na’urar sadarwa, rigar ruwa, bargo, layu da sauran kayayyaki.
Laftanal Kanal Sani Uba ya ce babban hafsan sojoji ya yaba da jajircewa, kwazo da dabarun da sojojin suka nuna a yayin aikin.
Ya ƙara da cewa nasarar wannan samame ta nuna yadda kokarin yaki da ta’addanci ke samun nasara, tare da tabbatar da aniyar rundunar OPHK na ci gaba da kai farmaki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a da dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.
Wasu sojoji sun hallaka 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ragargazar 'yan bindiga a jihar Kebbi.
Sojojin sun hallaka 'yan bindiga sama da 80 bayan sun yi arangama da su a karamar hukumar Ngaski ta jihar.
Hakazalika, sojojin sun kwato babura tare da kubutar da mutanen da 'yan bindigan suka yi garkuwa da su
Asali: Legit.ng


