Bulama Bukarti Ya Kawo Mafita ga Najeriya maimakon Sauya Hafsoshin Tsaro
- Masanin tsaro, Bulama Bukarti ya ce sauya shugabannin rundunonin tsaro ba zai magance ta'addanci ba
- Ya ce sauyin da Bola Tinubu ya yi ba shi ne mafita ba sai an sake fasalin dabarun yaki da hanyoyin inganta tsaro a kasa
- Bukarti ya ce a halin yanzu Najeriya tana bukatar sababbin dabaru da tunani, ba wai sauya mukamai kawai ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Masanin tsaro, Bulama Bukarti, ya ce Najeriya ba za ta iya shawo kan matsalolin ta'addanci ba ta hanyar sauya hafsoshin tsaro kawai ba.
Dr. Bulama Bukarti ya ce idan ana son magance matsalar, dole sai an yi sauye-sauyen tsarin tsaron kasa gaba ɗaya ba.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels Television, inda ya yi tsokaci kan sauyin manyan hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar kwanan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukarti ya ce wannan sauyi ba sabon abu ba ne a tarihin kasar, domin an taba yin irinsa a baya amma babu wani sauyi mai ma’ana da ya biyo baya saboda rashin tsari da sababbin dabaru.
“Hafsoshin tsaro kwararru ne,” Bukarti
A cewar Bukarti, sababbin hafsoshin da aka nada duk suna da kwarewa da cancanta, amma matsalar ita ce yadda tsarin tsaron Najeriya yake.
The Cable ta rahoto ya ce:
“Dukkan sababbin hafsoshin tsaro sun cancanci mukamansu idan aka duba tarihin aikinsu da kwarewarsu, amma matsalar ita ce tsarin da suke aiki a ciki.
“Mun sha ganin sauya shugabannin tsaro a baya, amma ba a ga wani babban sauyi ba saboda babu garambawul a tsarin.
"Sauya shugabanni ba zai magance matsalar ba idan tsarin bai canza daga yadda yake ba.”

Source: Facebook
Me ake bukata domin inganta tsaro?
Bulama Bukarti ya kara da cewa matsalar Najeriya ba rashin cancantar shugabannin tsaro ba ce, sai dai rashin shirin sauya tunani da dabarun yaki da ta’addanci.
Ya ce:
“Ba cancanta ba ce ke magance matsalar tsaro. Tambayar ita ce: shin sababbin shugabannin suna da jajircewar yin garambawul?
“Tsawon shekaru uku da suka gabata, ba mu ga wani canji a falsafar yaki da ta’addanci ba. Dole ne a sake duba dabarun yaki idan ana son samun nasara.”
Bulama Bukarti ya bukaci a yi gyara
Bukarti ya jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da fama da matsalolin tsaro muddin sauya shugabanni ake kawai ba tare da gyaran tsarin ba.
“Ba sauyi ake bukata ba, ana bukatar garambawul. Idan ba haka aka yi ba, za mu ci gaba da zama a wuri guda ba tare da ci gaba ba,”
Inji shi.
Martanin ADC kan sauya hafsoshin tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta yi magana kan sauya shugabannin tsaro da Bola Tinubu ya yi.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya soki sauyin yana cewa an dauki matakin cikin gaggawa a lokacin da ake rade-radin juyin mulki.
Kakakin jam'iyyar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta fayyace dalilan sauyin domin kada a ci gaba da yada jita-jita da ke iya tada hankulan jama’a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


