Kwana Ya Kare: Babbar Jami'a a Rundunar Yan Sanda Ta Rasu bayan An Mata Tiyata

Kwana Ya Kare: Babbar Jami'a a Rundunar Yan Sanda Ta Rasu bayan An Mata Tiyata

  • DPO ta yan sandan caji ofis na Festac , CSP Matilda Ngbaronye ta riga mu gidan gaskiya bayan an mata tiyata a jihar Legas
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Legas, SP Abimbola Adebisi ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar
  • Kwamishinan 'yan sanda ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar, wacce aka bayyana da jajirtacciya da ta iya mu'amala da jama'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Najeriya – Rundunar ’yan sandan jihar Lagos ta tabbatar da rasuwar Babban Jami’ar ’Yan Sanda, CSP Matilda Ngbaronye.

Kara karanta wannan

Jami'ar FUDMA ta samu sabon shugaba bayan tantance farfesoshin da ke takara

CSP Ngbaronye, wacce ta kasance Divisional Police Officer (DPO) ta caji ofis din Festac, ta rasu ne bayan an mata tiyatar fibroid a jihar Legas.

Jami'ar yan sanda.
Hoton DPO ta rundunar yan sanda da ke aiki a Legas, CSP Matilda Ngbaronye Hoto: Owolabi W. Temitope
Source: Facebook

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa CSP Ngbaronye ta rasu ne ranar 24 ga Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe 11:30 na dare a asibitin Mayriamville Medical Centre da ke Surulere.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun tabbatar da rasuwar DPO

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Lagos, SP Abimbola Adebisi, ya tabbatar da labarin, yana mai cewa marigayiyar ta rasu bayan an kammala mata tiyata.

A cewar kakakin rundunar yan sandan:

“Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Lagos na bakin cikin sanar da rasuwar DPO ta ofishin Festac, CSP Matilda Ngbaronye.
"Ta rasu ne bayan tiyata da aka yi mata a asibitin Mayriamville Medical Centre, Bode Thomas, Surulere, ranar Juma’a 24 ga Oktoba, 2025.”

Mutuwar Ngbaronye ta girgiza yan sanda

Rundunar yan sanda ta kara da cewa ta yi babban rashi na wata jajirtacciyar jami’a mai gaskiya da kwazo, wacce ta yi aiki da cikakken sadaukarwa da mutunci.

Kara karanta wannan

Jagororin PDP sun rabu a kan bai wa turaki shugabancin jam'iyya

"Har zuwa rasuwarta, kowa ya san CSP Ngbaronye jami'a ce mai ƙwazo, ladabi da bin doka wajen gudanar da aikinta.
"Halayenta na kirki da yadda take mu’amala da jama’a sun taimaka sosai wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’umma. Labarin rasuwarta ya girgiza dukkanin rundunar," in ji Adebisi.

Kwamishinan yan sanda ya yi ta'aziyya

Sanarwar ta kara da cewa kwamishinan yan sandan Legas, CP Olohondare Jimoh, tare da dukkan jami’ai da ma’aikata, suna mika ta’aziyyarsu ga iyalinta da mahaifiyarta.

"Kwamishina ya riga ya tuntubi mijinta da ɗan’uwanta wanda malamin addini ne, domin mika sakon ta’aziyya da tallafin rundunar a wannan lokaci mai raɗaɗi.”
Sufeta Janar na rundunar yan sandan Najeriya.
Hoton Sufetan Yan Sanda na kasa, IGP Kayode a ofis Hoto: @policeNG
Source: Twitter

Vanguard ta tattaro cewa za a ayyana cikakken jadawalin jana’izarta nan ba da jimawa ba.

“Allah Ya jikanta da rahama, Ya ba iyalinta da abokan aikinta haƙuri da juriya,” in ji SP Adebisi.

An kama wanda ya kashe John Zuya

A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda a karamar hukumar Tafawa Balewa ta jihar Bauchi sun kama wani mutum da ake zargi da hannu a kisan mawaki, John Zuya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bayyana dalilin cafke Omoyele Sowore a kotu

Rahotanni sun nuna cewa Zuya ya rasu cikin yanayi mai cike da rudani bayan dawowarsa daga Lagos, inda ya halarci wani gagarumin taro.

Mutuwarsa ta haifar da tashin hankali da jimami a tsakanin ‘yan uwansa da mazauna yankin, inda mutane da dama ke neman a tabbatar da adalci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262