Gwamna Radda Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, an Sauyawa Kwamishinoni Ma'aikatu

Gwamna Radda Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, an Sauyawa Kwamishinoni Ma'aikatu

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi garambawul gwamnatinsa domin inganta harkokin mulki
  • Dikko Umaru Radda ya sauya wasu kwamishinoni ma'aikatun da za su jagoranta, su sauke nauyin da aka dora musu
  • Hakazalika, gwamnan ya nada sababbin masu ba shi shawara na musamman a wani mataki na kara inganci a aikin gwamnati

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gudanar da babban sauyi a majalisar zartarwa ta jihar.

Gwamna Radda ya canza ma’aikatu ga wasu kwamishinoni tare da nada sababbin masu ba shi shawara guda biyu, domin karfafa ingancin aiki da kyautata gudanar da mulki a fadin jihar.

Gwamna Radda ya yi garambawul a gwamnati
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahima Kaulaha Mohammed, ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Jumma'a, 24 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Kwamishina mai ci a Gombe ya yi bankwana da duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya yi garambawul

Ibrahima Kaulaha Mohammed ya bayyana cewa sauyin zai fara aiki nan take, kuma an tsara shi ne domin daidaita manufar gwamnatin jihar da tsarin (Building Your Future Agenda).

A cikin sauyin, Hon. Adnan Nahabu ya zama kwamishinan ilmi na manyan makarantu, koyon sana’o’i da fasaha.

Farfesa Ahmad Muhammad Bakori, wanda a baya yake rike da ma’aikatar noma da ci gaban dabbobi, yanzu zai jagoranci sabuwar ma’aikatar ci gaban dabbobi.

Hon. Aliyu Lawal Zakari an mayar da shi daga ma’aikatar matasa da wasanni zuwa ma’aikatar noma.

Hajiya Zainab Musa Musawa an sauya ta daga kwamishiniyar ma’aikatar ilmin firamare da sakandare zuwa ma’aikatar harkoki na musamman.

Hon. Yusuf Suleiman Jibia ya zama kwamishinan ilmin firamare da sakandare yayin da Injiniya Surajo Yazid Abukur ya zama kwamishinan matasa da wasanni.

Hajiya Aisha Aminu, tsohuwar darakta a hukumar KASEDA, yanzu ita ce kwamishiniyar harkokin mata.

Kara karanta wannan

Injiniyoyi sun ga kokarin Gwamna Abba, sun ba shi lambar girmamawa

Radda ya nada masu bada shawara

Gwamna Radda ya kuma amince da nadin, Hajiya Hadiza Abubakar Yar’Adua a matsayin mai bada shawara kan abinci mai gina jiki da kula da jin kai.

Isa Muhammad Musa a matsayin mai bada shawara kan al’adu da fahimtar zamantakewa.

Gwamna Radda ya sauyawa kwamishinoni ma'aikatu
Dikko Umaru Radda na jawabi a wajen wani taro Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Radda ya taya su murna

Gwamna Radda ya taya sababbin kwamishinonin murna, yana mai jaddada cewa mukaman ba lada ba ne, sai dai kiran yin sabuwar hidima ga al’umma.

“Wannan sauyin da muka yi yana daga cikin matakanmu na inganta hadin kai, karfafa kwarewa, da hanzarta isar da shirye-shiryen gwamnati a fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, bunkasa matasa, karfafa mata, da jin dadin jama’a."

- Gwamna Dikko Radda

Gwama Radda ya nuna kwarin gwiwar cewa sabon tsarin zai kara kuzari da inganci a aikin gwamnati, tare da karfafa damar gwamnatin jihar wajen biyan bukatun al’ummar Katsina.

Wani mazaunin jihar Katsina, Abubakar Shitu ya nuna fatan cewa sauyin da gwamnan ya yi zai amfani mutanen jihar.

Kara karanta wannan

An yi rashin dattijo: Tsohon sakataren gwamnati ya rasu yana da shekaru 104

"Na ji dadin wannan sauyin musamman na Hajiya Zainab Musa Musawa, saboda ban ji dadin tsare-tsaren da take bullowa da su a ma'aikatar ilmi."
"Muna fatan Allah ya sa sauyin ya amfani mutanen jihar Katsina."

- Abubakar Shitu

Matsayar Radda kan sulhu da 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sake jaddada matsayarsa kan batun sulhu da 'yan bindiga.

Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da 'yan bindiga masu kai hare-hare ba.

Sai dai, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta goyi bayan yarjejeniyar zaman lafiya da al'ummomi suka kulla don samun zaman lafiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng