Gwamna Zulum Ya Koka kan Sabon Ta'addancin 'Yan Boko Haram a Borno
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya koka kan yadda 'yan Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare
- Zulum ya nuna cewa 'yan ta'addan na Boko Haram na amfani da jirage marasa matuka wajen kai hare-haren ta'addanci
- Gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki domin tabbatar da tsaron kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gudanar da binciken gaggawa da sake duba tsarin tsaron sama da na kasa.
Gwamna Zulum ya yi kiran ne bayan ’yan ta’addan Boko Haram sun yi amfani da jirgi marasa matuki mai dauke da makami wajen kai hari ga sansanin sojoji a jihar.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a garin Mafa, ranar Jumma’a, 24 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Zulum ya ce kan Boko Haram?
Gwamna Zulum ya nuna matukar damuwarsa kan sabon salo da ’yan ta’addan suka fara amfani da shi, abin da ya bayyana a matsayin mataki mai hatsari da ke barazana ga tsaron kasa baki daya.
“Abin da nake son na jaddada shi ne batun jirage marasa matuka. Wannan abu ne mai tayar da hankali. A garin Dikwa ma an gaya min cewa sun yi amfani da jirgi marasa matuki wajen kai hari."
"Yawaitar amfani da jirage marasa matuka, musamman a hannun kungiyoyin da ba na gwamnati ba, babban barazana ce ga kasar nan. Dole ne mu dauki mataki cikin gaggawa domin dakatar da yaduwar wannan al’amari."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Gwamnan ya bayyana cewa nasarar ’yan ta’addan wajen amfani da jirgi marasa matuki don kai hari ga dakarun sojoji ta tona asirin raunin tsaron sama da ke bukatar kulawar gaggawa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.
“Ba batun jihar Borno ba ne kawai, wannan barazana ce kai tsaye ga tsaron kasa. Dole mu karfafa iyakokin kasarmu, mu kuma karfafa tsarin tsaron sararin samaniyar kasa. Wannan lamari ne da ya kamata a dauka da muhimmanci."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Wace shawara Zulum ya bada?
Gwamna Zulum ya kara da cewa lokaci ya yi da hukumomin tsaro za su sake duba tsarin su sosai domin karfafa ikon kare sararin samaniya daga irin wannan sabon salon ta’addanci.
“Wannan lokaci ne da ya dace a duba yadda za a karfafa tsaron sama domin dakile amfani da jirage marasa matuka a hannun ’yan ta’adda."
- Gwamna Babagana Umara Zulum

Source: Twitter
Gwamna Zulum ya yabawa sojoji
Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun sojojin Najeriya bisa jajircewar su wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yi kira ga al’umma su rinka bada bayanai masu inganci ga jami’an tsaro idan sun ga ayyukan da ake zargin na da alaka da ta’addanci a yankunansu.
'Yan Boko Haram sun kai munanan hare-hare
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kai hare-haren ta'addanci a jihohin Borno da Yobe.
Tsagerun 'yan ta'addan sun kona motoci tare da sace makamai masu yawa bayan sun yi arangama da dakarun sojoji.
Garuruwan da aka kai hare-haren sun haɗa da Mafa, Dikwa, Marte da Ajiri a jihar Borno, sai kuma Katarko da ke jihar Yobe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


