Matasa Sun Yi Sallah da Addu'o'i kan cikar Seyi Tinubu Shekara 40 a Kano

Matasa Sun Yi Sallah da Addu'o'i kan cikar Seyi Tinubu Shekara 40 a Kano

  • Wata kungiyar matasan Arewa ta gudanar da addu’a na musamman a Kano don murnar cikar Seyi Tinubu shekara 40 a duniya
  • An gudanar da addu’ar ne a Masallacin Ansarudeen da ke Sabon Gari, Kano, tare da halartar matasa da dama daga Arewa
  • Shugabannin addini da matasa sun yaba da gudunmuwar dan shugaban kasar wajen karfafa matasa da ayyukan jin kai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Wasu matasan Arewa karkashin kungiyar Youth Alliance for Northern Development sun yi addu’a a ranar Juma’a domin murnar cikar Seyi Tinubu shekara 40 da haihuwa.

Rahoto ya nuna cewa an gudanar da addu’ar ne a Masallacin Ansarudeen da ke titin Sanusi, Sabon Gari, Kano.

Addu'ar Seyi Tinubu a Kano
Yadda aka yi sallah domin cikar Seyi Tinubu shekara 40. Hoto: Prime Time
Source: Facebook

Rahoton The Nation ya nuna cewa matasa da dama daga sassa daban-daban na Arewa ne suka halarci taron domin nuna soyayya da godiya ga Seyi Tinubu.

Kara karanta wannan

Sauya kundin mulki: Majalisa ta fara bitar bukatun kirkirar jihohi 55 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta kuma bayyana shirinta na gudanar da gagarumin bikin tunawa da ranar haihuwar Seyi Tinubu a cikin birnin Kano a ranar Asabar.

Addu’a da aka yi wa Seyi Tinubu a Kano

Sheikh Abdullateef Oyebamiji Emiabata ya jagoranci addu’o’in neman tsawon rai da lafiya ga Seyi Tinubu.

Malamin ya kara da rokon Allah Ya ci gaba da ba shi damar inganta rayuwar matasa da karfafa hadin kai a tsakanin ‘yan Najeriya.

Dan shugaban kasa Bola Tinubu
Seyi Tinubu na wani jawabi a taro. Hoto: Aso Rock Villa
Source: Twitter

Ya karanta wasu ayoyi daga Alƙur’ani mai girma, inda ya yi addu’a ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa da dorewar zaman lafiya.

Kungiyar matasa ta fadi dalilin addu'ar

Da yake zantawa da manema labarai bayan addu’ar, mai shirya taron, Seyi Olorunsola, ya ce addu’ar wani ɓangare ne na jerin shirye-shiryen bikin cika shekara 40 na Seyi Tinubu.

Ya ce:

“Muna murnar zagayowar ranar haihuwar Seyi, wanda duk da ba ya rike da wani mukamin siyasa, ya kasance ginshikin cigaban matasa da ayyukan jin kai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Injiniyoyi sun ga kokarin Gwamna Abba, sun ba shi lambar girmamawa

"Yana taimakawa marasa karfi da kuma karfafa ilimi ga matasa da dama.”

Olorunsola ya kara da cewa Seyi ya zama abin koyi ga matasan Najeriya masu neman ci gaba da mutunta ƙasa.

Jaridar Aminiya ta wallafa wasu daga cikin hotunan masu addu'ar suna sallah a shafinta na Facebook.

An yaba da gudunmuwar Seyi Tinubu

Daya daga cikin shugabannin matasan Arewa, Isyaku Rabi’u, ya ce an shirya bikin ne domin nuna godiya ga irin kokarin Seyi wajen samar da damammaki ga matasa, musamman a yankin Arewa.

Ya ce:

“Seyi ya taimaka wajen tabbatar da samar da mukamai 50 ga matasa, musamman daga Arewa, don haka muka ga dacewar mu nuna masa godiya da bikin cika shekara 40 da haihuwarsa.”

Gwamnati za ta sama wa matasa aiki

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Najeriya ta kaddamar shirin NJFP 2.0 domin samawa matasa aiki.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya kaddamar da shirin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a za su yi karatu kyauta saboda tallafin gwamna Umaru Bago

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa shirin ya samu goyon bayan kungiyar tarayyar Turai kuma matasa 20,000 ne za su amfana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng