Dangote Ya Taka Sabon Matakin Arziki a Duniya, Ya Mallaki Naira Tiriliyan 43.8
- Alhaji Aliko Dangote ya zama dan Afrika na farko da dukiyarsa ta kai dala biliyan 30 a jerin attajiran duniya da Bloomberg ya fitar
- Ya koma matsayi na 75 a jerin attajirai 100 na duniya, wanda Aliko Dangote ne kadai dan Afrika a wannan rukuni cikin masu kudi
- Nasarar ta zo ne bayan bude sabuwar masana’antar siminti ta Dangote a ƙasar Côte d’Ivoire da kuma habakar mai a matarsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Attajiri dan Najeriya kuma shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya kafa sabon tarihi bayan dukiyarsa ta kai dala biliyan 30 (₦43.8trn) a ranar Juma’a, 24, Oktoba, 2025.
Dangote, wanda shi ne attajiri mafi arziki a nahiyar Afrika, ya kara dala biliyan 2.25 cikin dukiyarsa, wanda hakan ya dauke shi zuwa matsayi na 75 a jerin manyan attajirai 100 na duniya.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta gano cewa Dangote ya kara samun matsayin ne a bisa rahoton da Bloomberg Billionaires Index ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da suka habaka arzikin Dangote
Wannan nasara ta zo ne mako biyu bayan kamfanin Dangote ya kaddamar da sabuwar masana’anta a Attingué, yankin masana’antu na Côte d’Ivoire.
Kamfanin ya ce masana’antar da ke da fili mai fadin hekta 50 na da karfin samar da tan miliyan uku na siminti a duk shekara.
Rahoton The Cable ya nuna cewa masana'antar simintin na daga cikin manyan kamfanonin da Dangote ya mallaka a wajen Najeriya.

Source: UGC
A gida kuwa, Dangote ya ci gaba da karfafa gwiwa a bangaren masana’antar mai, tun bayan fara aiki da matarsa ta tace fetur mai darajar biliyoyin daloli da ke Ibeju-Lekki a Legas.
Ya bude matatar mai din a watan Mayu, 2023, wacce ke da karfin tace ganga 650,000 na mai a rana, a fili mai fadin hekta 2,635 a Legas.

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
Yadda matatar Dangote ke aiki
Matatar man ta fara tace dizal a ranar 12, Janairu, 2024, sai dai samar da fetur bai fara ba sai 3, Satumban 2024, saboda kalubalen samar da danyen mai.
Bayan fama da kalubale daga kungiyoyin man fetur kan shiri raba mai kyauta, matatar ta cigaba da tace mai a Najeriya.
Haka kuma, matatar Dangote na shirin kara karfin tace mai zuwa ganga miliyan 1.4 a rana, wanda zai wuce karfin matatar Jamnagar da ke Indiya da sauran matatun duniya.
Dangote zai sayar da hannun jarin matatarsa
A wani rahoton, kun ji cewa Dangote ya bayyana cewa yana da shirin saka hannun jarin matatarsa a kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX) a shekara mai zuwa.
Ya ce wannan tsari yana kama da wanda ya yi wa kamfanonin siminti da sukari da ya mallaka domin kara fadada kasuwancin su da bude damar shiga ga jama’a.
Dangote ya kuma bayyana cewa kamfanin NNPCL zai iya kara hannun jarinsa a matatar bayan kammala matakin farko na ci gaban aikin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
