Sauya Kundin Mulki: Majalisa Ta Fara Bitar Bukatun Kirkirar Jihohi 55 a Najeriya
- Majalisar dattawa ta tabbatar da aniyar yin gyare-gyaren da za su amfanar da al’umma a kundin tsarin mulki na 1999
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana matakan da ake dauka a halin yanzu
- A taron bitar kwana biyu da aka gudanar a Legas, an tattauna kan bukatun kirkirar jihohi, gundumomi da sauransu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas – Majalisar Dattawa ta tabbatar da cewa tana da cikakken shiri na gudanar da gyare-gyaren da za su tabbatar da kundin tsarin mulki da zai amfani 'yan kasa.
Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa ya bayyana haka ne a wajen taron hadin gwiwa na kwamitocin majalisa da ke duba kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka gudanar a Legas.

Kara karanta wannan
Akwai yiwuwar mata su karu a majalisa, gwamnoni sun goyi bayan kudiri na musamman
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau ya bukaci ‘yan majalisa da su tabbatar da cewa an kammala jerin gyare-gyaren farko kuma an mika su ga majalisun jihohi kafin karshen shekarar 2025.
Ana neman kirkirar jihohi 55 a Najeriya
Taron, wanda aka shirya domin yin nazari kan shawarwarin gyare-gyare da ake son yi, ya kunshi muhimman batutuwa da suka hada da bukatar samar da sababbin jihohi da gundumomi.
Rahotanni sun nuna cewa a yayin taron, an tattauna kan jimillar bukatun da suka hada da kudirin gyara 69, bukatun kirkirar jihohi 55.
Vanguard ta rahoto cewa akwai bukatun daidaita iyakoki guda biyu, da bukatun kirkirar sababbin kananan hukumomi 278.
Sanata Barau ya bayyana cewa an dauki tsawon shekaru biyu ana wannan aikin tare da samun shawarwari daga jama’a da kungiyoyin farar hula, cibiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki.
Barau ya nemi hadin kai da kishin kasa
Sanata Barau, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan gyaran kundin tsarin mulki, ya ce kwamitin zai duba batutuwan da aka gabatar.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta ce Najeriya ta zama abin koyi a kula da 'yan gudun hijira
Baya ga haka, Barau Jibrin ya bayyana cewa za a ba da shawarwari da kwamitin zai gabatar ga ‘yan majalisa a majalisun kasa biyu.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa, duk da gajeren lokaci, yana da yakinin cewa za a iya cimma matsaya cikin nasara idan aka yi aiki da hadin kai da kishin kasa.
A cewarsa:
“Mun zo daga bangarori daban-daban na kasa masu bambancin kabila, addini, da tattalin arziki, amma wannan kundin tsarin mulki shi ne ginshikin hadin kan Najeriya.
Dole ne mu yi wannan aiki da kishin kasa a matsayin abin da ya fi muhimmanci.”
Sanata Barau, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalisar ECOWAS, ya yi kira ga ‘yan majalisa da su guji muhawarar da za ta rika jawo rarrabuwar kawuna.
Majalisa na son sauya dokar EFCC
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta yi karatu na biyu ga kudirin neman sauya dokokin hukumar EFCC.
Majalisar ta bayyana cewa zamani ya sauya sosai, musamman a harkar kudi amma har yanzu dokokin hukumar ba su sauya ba.
Wani muhimmin gyara da majalisar ke son yi shi ne cire ikon da shugaban kasa ke da shi wajen sauya shugaban EFCC kai tsaye.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
