Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Najeriya Ta Zama Abin Koyi a Kula da 'Yan Gudun Hijira

Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Najeriya Ta Zama Abin Koyi a Kula da 'Yan Gudun Hijira

  • Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa Najeriya ta dauki matakan magance matsalolin ‘yan gudun hijira na cikin gida
  • Hakan na zuwa ne bayan kammala taron majalisar dinkin duniya na kwana uku a Najeriya inda aka yaba da kokarin gwamnati
  • An nemi kungiyoyin kasa da kasa da su kara taimako don samar da mafita ta dindindin ga wadanda rikice-rikice suka shafa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Majalisar Dinkin Duniya ta yaba wa gwamnatin Najeriya kan yadda ta tashi tsaye wajen magance matsalolin da ‘yan gudun hijira na cikin gida ke fuskanta a sassan kasar.

Wannan yabo ya fito ne daga kakakin sakataren majalisar, Stéphane Dujarric, yayin da yake jawabi a taron manema labarai bayan kammala ziyarar manyan jami’ansu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisar Tarayya za ta shiga cikin lamarin karin kudin gidan haya

'Yan gudun hijira
Wani dan gudun hijira na gyara sansaninsa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa jami’an kungiyoyi uku na majalisar; OM, UNHCR da UNDP sun gudanar da ziyarar kwanaki uku domin tattaunawa da gwamnati da masu ruwa da tsaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

UNHCR, hukumomin UN sun yabi Najeriya

Babban kwamishinan UNHCR mai kula da ayyukan taimako, Raouf Mazou, ya ce Najeriya ta taka rawar gani wajen sauya tsarin taimakon gaggawa zuwa hanyar dogaro da kai.

Haka kuma, jami’an majalisar sun bayyana cewa Najeriya ta ci gajiyar taimakon da UN ke bayarwa wajen samar da bayanai da tsarin manufofi a matakin jihohi.

Daraktar ofishin UNDP mai kula da harkokin rikici, Shoko Noda ta ce Najeriya na da damar zama abin koyi ga sauran kasashe wajen samar da mafita ga ‘yan gudun hijira.

UN ta kafa cibiyar bayanai a Yobe

Hukumar IOM ta bayyana cewa ta kafa cibiyar bayanai a jihar Yobe domin taimaka wa gwamnati wajen tarawa da sarrafa bayanai game da ‘yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ICAN ta yi hangen nesa, ta gano babbar barazana ga darajar Naira

Cibiyar za ta taimaka wajen nazari da fitar da rahotanni bisa hujjoji, don karfafa yanke shawarar da za ta tabbatar da farfadowar tattalin arziki da zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa.

Sansanin 'yan gudun hijira
Wani sansanin 'yan gudun hijira a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Aikin yana karkashin shirin IDS-Fund, wanda ke inganta tsarin gwamnati wajen magance matsalolin 'yan gudun hijira a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Bukatar karin goyon bayan kasa da kasa

Rahotannin UN sun nuna cewa Najeriya tana da sama da mutum miliyan 3.5 da ke zaune a matsayin ‘yan gudun hijira a cikin kasar, sakamakon rikice-rikice da rashin tsaro.

Wadanda suka halarci ziyarar sun hada da Ugochi Daniels daga IOM, Raouf Mazou na UNHCR da Shoko Noda daga UNDP, inda suka gana da jami’an gwamnati, sarakuna da kungiyoyin farar hula.

Rahoton Arise News ya nuna cewa sun bukaci kungiyoyin kasashen waje da cibiyoyin kudi na duniya da su ci gaba da tallafawa Najeriya.

Najeriya ta yi martani kan harajin Trump

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi martani kan harajin da shugaban Amurka, Donald Trump ya kakaba wa Najeriya.

Kara karanta wannan

Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya ce harajin ba lallai ya yi tasiri kan Najeriya ba.

Yusuf Tuggar ya kara jaddada cewa Najeriya ba za ta karbi bakin da shugaba Donald Trump zai kora daga Amurka ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng