Farashin Buhun Shinkafa, Masara, Wake, Ya Ruguzo Kasa a Kasuwannin Abuja
- Farashin kayan abinci kamar shinkafa, wake, dawa, masara, gero da garin rogo ya ragu da kusan kashi 50 cikin 100 a yankunan Abuja
- ‘Yan kasuwa sun bayyana cewa raguwar ta samo asali ne daga samun damina mai albarka da kuma karancin kudi a hannun jama’a
- A wasu yankuna kamar Abaji, Gwagwalada, buhun masara da dawa sun ragu daga N35,000 zuwa tsakanin N18,000 da N25,000
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Farashin kayan abinci ya cigaba da yin kasa a kasuwannin karkara na babban birnin tarayya Abuja.
Saukar farashin ya sanya masu saye da sayarwa na nuna farin ciki da fatan farashin zai ci gaba da sauka da kaka.

Source: Facebook
Daily Trust ta ce kayan abinci da suka hada da shinkafa, wake, dawa, gero, masara, garin rogo da doya sun ragu da kashi 50 cikin 100 a wasu kasuwanni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Raguwar farashi a kasuwar Abaji
Rahoton daga kasuwar Abaji ya nuna cewa mudun shinkafar gida da ake sayarwa tsakanin N2,000 da N1,800 a wata biyu da suka gabata, yanzu ana sayar da shi tsakanin N1,500 da N1,300.
Haka kuma, mudun masara wanda ya kai N800 a baya yanzu ya koma tsakanin N350 da N400, yayin da mudun farin wake ya ragu daga N2,500 zuwa N2,000.
Bincike ya nuna cewa doya guda biyar wanda a baya ake siyarwa tsakanin N10,000 zuwa N15,000, yanzu suna tsakanin N4,000 da N7,000 gwargwadon girmansu.
Farashi a kasuwannin Kwali da Kwaita
A kasuwar Kwaita da ke Kwali, inda ake kasuwa duk bayan kwana hudu, mudun shinkafa yanzu yana tsakanin N1,100 da N1,200.
Haka mudun wake ya ragu daga N2,500 zuwa N2,000, inda nau’in farin wake kanana yake tsakanin N1,400 da N1,600.

Source: UGC
Wani dillali, Malam Garba Abdullahi, ya ce:
“A bana, manoma sun samu amfani mai yawa sosai, amma kuma karancin kudi a hannun jama’a yana daga cikin dalilan da suka sa farashin kayan abinci ke sauka.”

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
Kasuwannin da suka fi saukin farashi a Abuja
A kasuwannin Paikon-Kore da Dobi da ke Gwagwalada, rahotanni sun nuna cewa farashin kayan abinci ya ragu da kusan kashi 65 cikin 100.
Wasu ‘yan kasuwa sun ce farashin hatsi kamar masara da dawa sun yi kasa fiye da yadda aka zato, inda masu siye daga wasu garuruwa ke zuwa da manyan motoci domin saye da yawa.
Wani dan kasuwa, Mathew Nyiste, ya bayyana cewa:
“Buhun masara da a baya ake sayarwa N30,000 yanzu yana tsakanin N18,000 da N20,000, yayin da buhun dawa ya ragu daga N35,000 zuwa N25,000.”
Dalilin saukar kayan abinci a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da suka jawo saukar farashin kayan gona.
Ministan noma, Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana haka yayin wani taro a birnin tarayya Abuja a makon da ya wuce.
Ya ce matakan da Bola Tinubu ya dauka na sauya fasalin tattali na cikin dalilan da kuma samun amfanin gona mai yawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
