Daliban Jami'a za Su Yi Karatu Kyauta saboda Tallafin Gwamna Umaru Bago

Daliban Jami'a za Su Yi Karatu Kyauta saboda Tallafin Gwamna Umaru Bago

  • Gwamnan jihar Neja ya bayar da umarnin karatu kyauta ga sababbin daliban Jami’ar Abdulkadir Kure da ke Minna
  • Umaru Bago ya ce an soke kudin karatu na shekarar 2024/2025 ga dalibai 809 da aka karɓa a wannan zangon
  • Ya sanar da soke shirin tura dalibai kasashen waje, yana mai cewa za a zuba kudin cikin cigaban jami’ar jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja – Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sanar da cewa sababbin daliban Jami’ar Abdulkadir Kure da ke Minna za su yi karatu kyauta a zangon karatun 2024/2025.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin bikin rantsar da sababbin daliban jami’ar 809, inda ya ce gwamnati ta soke duk wani kudin karatu domin tallafa wa ilimi da inganta harkar makarantur.

Kara karanta wannan

Injiniyoyi sun ga kokarin Gwamna Abba, sun ba shi lambar girmamawa

Gwamnan Neja a AKUM
Gwamna Umaru Bago da shugabannin jami'ar AKUM. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da gwamnan ya yi ne a wani sako da hadiminsa, Balogi Ibrahim ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umaru Bago ya bayyana cewa za a ware 2% na hannun jarin jihar a sanya a asusun tallafi na jami’ar, domin tabbatar da dorewar ci gaban ilimi a matakin gaba.

Bago ya soke shirin tura dalibai ketare

Gwamna Bago ya ce gwamnatin jihar ta fasa shirin tura dalibai kasashen waje domin neman ilimi, saboda an yanke shawarar mayar da wannan kudi wajen bunkasa jami’o’in cikin gida.

A cewarsa:

“Ba laifi ba ne idan shugaba ya canza shawara. Mun taba tsara tura wasu dalibai kasashen waje, amma yau na soke wannan shiri.
"Zan fi son mu zuba wannan kudi a cikin jami’ar mu.”

Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen bunkasa ilimi da kayan aiki a jami’ar, tare da bai wa dalibai damar samun ingantaccen ilimi a cikin gida.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ICAN ta yi hangen nesa, ta gano babbar barazana ga darajar Naira

Gwamna Bago ya ba dalibai N100,000

Gwamnan ya kara da cewa gwamnati za ta gina gidaje ga malamai da ma’aikatan jami’ar, sannan za a fara koyar da fannin likitanci daga zangon karatu na gaba.

Ya kuma taya sababbin daliban murna bisa samun nasarar shiga jami’ar, tare da kiransu da su zama jakadun kirki ga iyalansu da jiharsu.

Daliban jami'ar AKUM a Neja
Wasu daga cikin daliban da aka rantsar a jami'ar AKUM. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Gwamnan ya kara da cewa kowane sabon dalibi zai samu tallafin kudi na N100,000 a matsayin kyauta daga gwamnatin jihar.

Jawabin shugaban jami’ar jihar Neja

Shugaban jami’ar AKUM, Farfesa Mohammed Aliyu Paiko, ya yaba da wannan mataki na gwamnati, yana mai cewa hakan zai kara karfafa sha’awar dalibai.

Farfesan ya kuma bayyana cewa jami’ar na shirin aiwatar da tsare-tsaren Gwamna Bago na tattalin arziki domin samar da kwararru a fannoni irin su noma, fasahar kere-kere, kimiyyar muhalli,

Hadarin tanka ya kashe mutane a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa mutanen jihar Neja jaje kan hadarin tankar mai.

Kara karanta wannan

Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji

Hakan na zuwa ne bayan hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 40 bayan motar ta kama da wuta.

Wasu bayanai sun ce hadarin ya rutsa da mutanen ne yayin da suke diban man fetur bayan motar ta yi hadari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng