'Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin Cafke Omoyele Sowore a Kotu

'Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin Cafke Omoyele Sowore a Kotu

  • Jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun yi caraf da tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore
  • Mai magana da yawun rundunar ya bayyana dalilin da ya sanya aka cafke Sowore a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa kamun da aka yi wa Sowore na da nasaba da zanga-zangar da ya.jagoranta don neman a saki Nnamdi Kanu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rundunar ’yan sandan Najeriya (NPF) ta yi bayani kan kamun da jami'anta suka yi wa Omoyele Sowore.

Rundunar 'yan sandan ta ce an kama shi ne domin tabbatar da adalci wajen gurfanar da duk wadanda suka shiga cikin zanga-zangar da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin.

'Yan sanda sun fadi dalilin cafke Sowore
Omoyele Sowore da kakakin rundunar 'yan sanda, Benjamin Hundeyin Hoto: @YeleSowore, @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan artabu mai zafi, sojoji sun dakile harin Boko Haram da ISWAP a jihohi 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun cafke Yele Sowore

An kama Sowore a ranar Alhamis a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, jim kadan bayan ya bayyana a wurin domin nuna goyon baya ga Nnamdi Kanu wanda ke tsare.

Sowore yana kan gaba wajen kiran a saki Kanu daga tsare, kuma a ranar Litinin ya jagoranci wata zanga-zanga a Abuja domin neman a saki shugaban na kungiyar IPOB.

Meyasa aka kama Sowore?

Benjamin Hundeyin ya ce Sowore, wanda ake zargi ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa wurin da aka haramta shiga yayin nuna goyon baya ga shugaban IPOB da ke tsare, Nnamdi Kanu.

'Dan sandan ya shaida cewa an kama shi ne domin tabbatar da cewa doka ta shafi kowa.

Ya bayyana cewa a ranar Litinin an kama mutane takwas a gaban Transcorp Hilton, Abuja, sannan aka kama karin mutane biyar a kusa da ma’aikatar kudi, wanda hakan ya kai adadin wadanda aka kama zuwa mutane goma sha uku (13).

Kara karanta wannan

Sowore: 'Yan sanda sun cafke tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya a kotu

“A yau rundunar 'yan sanda ta kama Omoyele Sowore. Kuna iya tambaya me ya sa aka kama shi. Dalilin a bayyane yake."
“Dukkan mutanen da aka kama sun bayyana cewa Sowore ne ya jagorance su zuwa wurin da aka hana shiga, wanda hakan ya saba da umarnin kotu."
"Idan muka gurfanar da su ba tare da wanda ya jagorance su ba, ba za a kira hakan adalci ba."

- Benjami Hundeyin

'Yan sanda sun yi magana kan cafke Omoyele Sowore
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore Hoto: @YeleSowore
Source: Facebook

Za a kai Sowore gaban kotu

Jami’in hulda da jama’a na rundunar 'yan sandan ya tabbatar da cewa Sowore ba zai dauki lokaci mai tsawo a tsare ba, domin an shirya gurfanar da shi gaban kotu ba tare da bata lokaci ba, rahoton The Nation ta zo da labarin.

“Kamar yadda aka yi da sauran, ba zai dauki fiye da awa 24 tare da mu ba. Da zarar an kammala shirin tuhumarsa, za mu gurfanar da shi gaban kotu. Idan komai ya tafi yadda ya kamata, za mu tabbatar da cewa yau din nan an kai shi kotu."

- Benjamin Hundeyin

Kara karanta wannan

Dakarun tsaron Najeriya sun harzuka, sun hallaka jagoran 'yan ta'adda a Filato

An kai karar Sowore gaban kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta maka tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, a gaban kotu.

Gwamnatin ta kai karar Sowore ne bisa tuhume-tuhume biyar da suka shafi wallafa sakon karya da cin mutuncin Shugaba Bola Tinubu a shafin sada zumunta.

Masu gabatar da kara sun zargi Sowore da yin amfani da shafinsa na X wajen wallafa sakon cin mutuncin Shugaba Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng