Sowore: 'Yan Sanda Sun Cafke Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasar Najeriya a Kotu
- 'Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, ya shiga hannun ‘yan sanda bayan ya jagoranci zanga-zangar ‘Free Nnamdi Kanu’ a Abuja
- An kama shi a harabar babbar kotun tarayya yayin da yake barin wurin shari’ar Nnamdi Kanu, kuma a gaban lauyoyinsa
- Lauyoyinsa sun bayyana cewa ‘yan sanda sun fada masu cewa suna bin umarnin kwamishinan rundunar ne na birnin Abuja
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An kama dan gwagwarmaya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja.
An rahoto cewa, 'yan sanda ne suka tare Sowore bayan fitowa daga cikin kotu a ranar Litinin, suka tafi da shi, bayan ya jagoranci zanga-zangar #FreeNnamdiKanu.

Source: Facebook
'Yan sanda sun kama Omoyele Sowore
Rahotan jaridar Daily Trust ya nuna cewa Sowore, wanda ya tsere lokacin da ‘yan sanda suka kama wasu masu zanga-zanga, ya sake bayyana a kotu don halartar shari’ar Nnamdi Kanu, inda aka kama shi shi ma.

Kara karanta wannan
Atiku da wasu manya na fafutukar fito da shi, shugaban IPOB ya rikita lissafin lauyoyi a kotu
A wani saƙo da Sowore ya wallafa a shafinsa na Facebook kafin kamun nasa, ya bayyana cewa babban lauyan Kanu, Kanu Agabi (SAN), zai janye daga kare shugaban IPOB, yana mai ikirarin cewa shari’ar “ta koma siyasa gaba ɗaya.”
“Na gana da Kanu Agabi a kotu, kuma ya tabbatar min cewa tawagarsu za ta janye daga shari’ar Nnamdi Kanu saboda siyasar da ke ciki,” in ji Sowore.
Da yake barin kotun, ‘yan sanda suka tare shi, suka bukace shi da ya bi su zuwa ofishinsu, inda daga ƙarshe ya amince ya tafi tare da su bayan ja-in-ja.
Wanda ya sa 'yan sanda suka kama Sowore
Wata majiya daga hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa an kama Sowore ne bisa umarnin Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya (Abuja), cewar rahoton Sahara Reporters.
“Kwamishinan ya gayyace shi tun farko, amma kafin ya isa ofishin su, sai suka yi gaggawar kama shi a kotu,” in ji wani abokinsa da ya nemi a sakaya sunansa.
Rahotannin sun nuna cewa, ya kamata a ce Sowore ya bayyana a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite kan tuhumar da 'yan sanda ke yi masa, amma alkalin bai zauna ba.

Source: Facebook
Lauyoyi sun kalubalanci kama Sowore
Tawagar lauyoyinsa karkashin jagorancin Tope Temokun ta kalubalanci jami’an ‘yan sanda a wurin, tana tambayar dalilin kamun ba tare da takarda daga kotu ba.
Sai dai jami’an 'yan sandan suka dage cewa suna bin “umarnin kwamishinan 'yan sanda ne kai tsaye, don haka aikinsu suke yi.
Sowore, wanda aka fi sani da jagorantar zanga-zangar #RevolutionNow, ya daɗe yana sukar manufofin gwamnati da kare hakkin ɗan Adam a Najeriya.
Sowore ya tsere wajen zanga-zangar sakin Kanu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sanda da wasu jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu da harsasai.
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ne ya jagoranci masu zanga-zangar a wasu sassa na birnin tarayya Abuja.
A wani bidiyo da Legit Hausa ta gani, an ga Sowore ya ranta a na kare yayin da ya ji yo karar harbe-harben bindiga, inda shi da mabiyansa suka nemi mafaka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
