Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Farashin Gidaje a Jihohi domin Jama'a su Mallaka

Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Farashin Gidaje a Jihohi domin Jama'a su Mallaka

  • Gwamnatin Tarayya ta amince da farashin bai daya ga dukkan gidajen shirin Renewed Hope a fadin kasa
  • An tabbatar da hakan ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar gidaje da raya birane ta fitar a Abuja a ranar Alhamis
  • Gwamnati Najeriya ta ce shirin zai bai wa ma’aikata da talakawa damar mallakar gida cikin sauki a kasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Najeriya – Ma’aikatar gidaje da raya birane ta bayyana cewa gwamnati ta amince da farashin bai daya ga dukkan gidajen da ke karkashin shirin Renewed Hope Estate.

Wannan mataki, a cewar ma’aikatar, na da nufin tabbatar da gaskiya, daidaito da saukin mallakar gida ga kowane dan kasa.

Gidajen Tinubu a Najeriya
Samfurin gidajen da gwamnatin Tinubu ta gina a Najeriya. Hoto: MINISTRY OF HOUSING & URBAN DEVELOPMENT
Source: Facebook

Vanguard ta ce sanarwar ta fito ne daga bakin jami'in yada labarai na ma’aikatar, Badamasi Haiba, wanda ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan artabu mai zafi, sojoji sun dakile harin Boko Haram da ISWAP a jihohi 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin gidajen gwamnatin Bola Tinubu

A cewar Badamasi Haiba, farashin da aka amince da su a dukkan jihohin Najeriya za su kasance kamar haka:

  1. Gida mai ɗaki ɗaya: ₦8.5m
  2. Gida mai ɗaki biyu: ₦11.5m
  3. Gida mai ɗaki uku: ₦12.5m

Ya ce wannan tsari zai tabbatar da adalci da saukin samun gida a dukkan yankunan kasar, inda kowane dan Najeriya zai samu damar mallaka ba tare da wariya ba.

Haiba ya kara da cewa wannan tsarin na daya daga cikin hanyoyin da gwamnati ke bi domin saukaka rayuwa da inganta walwalar al’umma.

Wadanda za a ba damar sayen gidajen

Ministan gidaje Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana cewa gwamnati za ta bai wa ma’aikata, masu matsakaicin karfi, da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje fifiko wajen samun gidajen.

Ya ce gwamnati tana son ganin cewa kowane mai son mallakar gida ya kasance yana da sana'ar da ya ke samun kudin shiga, domin tabbatar da gaskiya da daidaito a tsarin.

Kara karanta wannan

ASUU ta janye yajin aiki a jami'o'i, ta kafa wa gwamnatin Tinubu sharadi

Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dangiwa ya bayyana wannan shirin a matsayin wani muhimmin bangare na manufofin gwamnatin Bola Tinubu na samar da sauki ga kowane dan kasa.

Hanyar biyan kudin mallakar gida

Babban sakataren ma’aikatar, Dr Shuaib Belgore, ya bayyana cewa an samar da hanyoyi daban-daban na biyan kudi don saukaka wa masu neman gidaje.

Ya ce akwai zaɓuɓɓuka kamar cikakken biyan kudi, tsarin lamuni (mortgage), tsarin biyan kudi a hankali, da kuma tsarin haya zuwa mallaka (rent-to-own).

Ya kara da cewa wadannan hanyoyi za su bai wa mutane damar mallakar gidaje ba tare da tsananin matsin tattalin arziki ba.

Yadda za a saye gidajen Tinubu

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa za a fara sayar da wadannan gidaje a yankunan Arewa da Kudu nan ba da jimawa ba.

Haka kuma, an ce za a iya neman gidaje ta shafin intanet na Renewed Hope Housing a www.renewedhopehomes.fmhud.gov.ng ko kuma a ofisoshin ma’aikatar a fadin kasa.

Kara karanta wannan

Kotu ta fadi dalilin dage zaman shari'ar kwamandojin 'Yan ta'addan Ansaru

Shirin ya zama wani ginshiki na gwamnati wajen tabbatar da walwala, da samar da muhalli mai inganci ga daukacin al’ummar Najeriya.

Saudi ta ba 'yan Najeriya damar sayen gida

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Saudiyya ta kawo dokar da ta ba 'yan Najeriya da wasu kasashe damar mallakar gida a Makkah.

Rahotanni sun nuna cewa a karkashin dokar, gwamnatin Saudiyya ta ba mutane damar sayen gida a kusa da Harami.

Baya ga gidaje, bincike Legit Hausa ya gano cewa dokar ta ba da damar mallakar kadarori da suka hada da otel a Makkah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng