Dangote zai Saka Sashen Matatarsa a Kasuwa, Mutane Za Su Saye Hannun Jari

Dangote zai Saka Sashen Matatarsa a Kasuwa, Mutane Za Su Saye Hannun Jari

  • Aliko Dangote ya bayyana shirin sayar da kaso tsakanin 5 zuwa 10 na hannun jarin matatar shi a kasuwar hannun jari ta Najeriya
  • Dangote ya ce shirin zai bi tsarin kamfanonin simintinsa da sukari, inda ya kara da cewa ba ya son mallakar fiye da kaso 70 na matatar
  • Ya tabbatar da cewa kamfanin na duba yiwuwar samun hadin gwiwa da masu saka jari daga Gabas ta Tsakiya domin fadada matatar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa matatarsa na shirin sayar da hannun jari tsakanin kaso 5 zuwa 10 a kasuwar hannun jari ta Najeriya (NGX) a shekara mai zuwa.

A cewar Dangote, wannan mataki zai biyo bayan irin tsarin da sauran kamfanoninsa suka bi, kamar na siminti da sukari domin karfafa amincewar masu saka jari.

Kara karanta wannan

Kanu: Dan ta'addan da aka rike ya jero gwamnoni, ministocin Tinubu, Buhari a shaidu

Alhaji Aliko Dangote
Dangote da wani sashe na matatar shi da ke Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Vanguard ta wallafa cewa Dangote ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da kamfanin S&P Global, inda ya ce shirin zai dogara da bukatar kasuwa da yanayin tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote zai sayar da sashen matatar shi

Dangote ya bayyana cewa manufarsa ita ce rage hannun jarin kamfanin zuwa tsakanin 65% zuwa 70%, inda ya ce za su rika sayar da hannun jari a hankali gwargwadon bukatar masu saka jari.

Ya kara da cewa kamfanin na tattaunawa da wasu masu saka jari daga Gabas ta Tsakiya domin taimakawa wajen fadada ayyukan matatar da kuma wani sabon shirin sinadarai a kasar China.

A cewarsa:

“Manufar kasuwancinmu za ta canza. Maimakon mallakar kaso 100, yanzu za mu samu abokan hulɗa daga kasashen waje.”

Hulɗar matatar Dangote da NNPCL

Dangote ya kuma nuna yiwuwar karin kaso ga kamfanin mai na kasa, NNPCL, wanda a baya ya rage hannun jarinsa zuwa kaso 7.2.

Kara karanta wannan

Zaben Kamaru: Matasa sun barke da zanga zanga, an yi arangama da 'yan sanda

Daily Trust ta rahoto cewa ya ce za a iya sake tattauna batun karin kaso bayan matakin gaba na fadada aikin matatar ya kammala.

Matatar Dangote
Wani sashe na matatar Dangote. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Dangote ya bayyana cewa:

“Ina son mu nuna abin da wannan matatar za ta iya yi, sannan daga baya za mu zauna mu tattauna.”

Shirin fadada matatar Dangote

Matatar Dangote, wadda ta fara aiki a shekarar 2024, na shirin kara yawan tace man daga ganga 650,000 zuwa ganga 700,000 a kowace rana kafin karshen wannan shekara.

Dangote ya kara da cewa burinsu na dogon lokaci shi ne su kai karfin tace ganga miliyan 1.4 a rana, wanda zai zarce matatar Jamnagar a Indiya wadda ke tace ganga miliyan 1.36.

Ya kuma bayyana cewa suna shirin kara samar da sinadarin polypropylene daga ton miliyan 1 zuwa 1.5 a shekara tare da bude sababbin ayyuka a fannoni.

Matatar Dangote ta fuskanci barazana

A wani rahoton, kun ji cewa attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana matsalolin da ya fuskanta a matatar shi.

Dangote ya bayyana cewa an yi yunkurin lalata wasu wurare a matatar da ke Legas amma ba a yi nasara ba.

Kara karanta wannan

NNPP ta fadi hadarin dawo da zaben 2027 zuwa 2026 a Najeriya

Daga cikin matsalolin da matatar ta fuskanta akwai yunkurin tayar da gobara ta hanyar yunkurin cinna wuta a wasu wurare.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng