Tirela Dauke da Buhunan Siminti Ta Markade Mutane a Kusa da Jami'a, An Rasa Rayuka

Tirela Dauke da Buhunan Siminti Ta Markade Mutane a Kusa da Jami'a, An Rasa Rayuka

  • An rasa rayuka da dama da wata tirela dauke da buhunan siminti ta sauka daga kan titi, ta fada kan mutane a jihar Ondo
  • Rahoto ya nuna lamarin ya faru ne a kusa da Jami’ar Adekunle Ajasin da ke Akungba Akoko, a karamar hukumar Akoko ta Yamma
  • Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum takwas a hatsarin, ta kuma gargadi direbobi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akungba Akoko, Ondo – Akalla mutane takwas sun rasa rayukansu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a daren Laraba a kusa da Jami’ar Adekunle Ajasin da ke jihar Omdo.

Kara karanta wannan

ASUU ta janye yajin aiki a jami'o'i, ta kafa wa gwamnatin Tinubu sharadi

Rahotanni sun bayyana cewa babbar motar mai dauke da buhunan siminti ta afka kan shagunan mutane a Akungba Akoko, a karamar hukumar Akoko ta Yamma a jihar.

Jihar Ondo.
Hoton taswirar jihar Ondo. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani ganau ya shaida wa jaridar The Cable cewa motar tirela ɗauke da siminti ta kauce daga hanya a kan titin Owo–Akungba–Ikare Akoko, ta afka wa shagunan gefen hanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda tirela ta murkushe mutane a Ondo

Ganau ɗin ya ce,

"Direban motar ya gaza sarrafa ta sakamakon lalacewar birki, ya kauce daga hanya ya afka wa shaguna, ya tattake mutane da dama har suka mutu nan take.”

Wani mazaunin yankin kuma ya tabbatar da cewa mutane biyar suka mutu nan take, yayin da wasu suka makale ƙarƙashin motar.

“Motar daga garin Ikare ta taso, ba mu san ko an buɗe titin ba, ko kuma motar ce ta karya abin da aka toshe titin da shi ta biyo hanyar.
"Mutane biyar sun mutu nan take, amma ba mu san adadin waɗanda suka makale a ƙarƙashin motar ba.”

Daga cikin waɗanda suka mutu akwai wata mata da ba a tantance sunanta ba mai juna biyu, wadda aka ciro gawarta daga ƙarƙashin motar bayan da haɗarin ya faru.

Kara karanta wannan

DSS ta gano jihohi 2 da 'yan ta'adda ke shirin kai sababbin hare hare

FRSC ta tabbatar da faruwar hatsarin

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa (FRSC) reshen Ondo, Samuel Ibitoye, ya tabbatar da cewa mutane takwas ne suka mutu, maza biyar, mata biyu da ɗa namiji guda ɗaya.

Ya ce motar ta murkushe katanga a gaban jami’ar kafin ta sauka daga hanya ta afka wa shagunan, in ji rahoton Leadership.

“Akalla mutane takwas suka mutu a haɗarin, ciki har da maza biyar, mata biyu da kuma yaro ɗaya. An kwashe gawarwakinsu zuwa dakin ajiyar gawa na asibitin yankin," in ji Ibitoye.
Hukumar FRSC.
Hoton motocin hukumar FRSC a kan titi a Najeriya Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

Kwamandan ya ja hankalin direbobi su tabbata motocinsu na cikin koshin lafiya kafin su kama hanya, tare da bin dokokin zirga-zirga domin kauce wa irin waɗannan mummunan haɗurra a nan gaba.

Mutum 22 sun mutu a hatsarin tirela a Neja

A wani labarin, kun ji cewa wata tirela dauke da gomman mutane ta gamu da hatsari a titin Lambata zuwa Lapai da ke jihar Neja.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane da yawa sun mutu da wata tanka ta yi bindiga a Najeriya

An rahoto cewa tirelar na dauke da dabbobi da kuma mutane 42 a lokacin da ta yi hatsari, inda mutane 22 suka mutu.

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Neja ta sanar da cewa mutane 20 da suka tsira a hatsarin, sun samu munanan raunuka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262