Kotu Ta Soke Zaben Kananan Hukumomi, Ta Tsige Ciyamomi 13 da Kansiloli 171

Kotu Ta Soke Zaben Kananan Hukumomi, Ta Tsige Ciyamomi 13 da Kansiloli 171

  • Babbar kotun tarayya da ke Abakaliki ta soke zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a watan Yuli 2024 a Ebonyi
  • Mai shari’a H.I.O. Oshomah ya ce EBSIEC ba ta bi ka’idojin dokar zabe ba, don haka ya tsige ciyamomi 13 da kansiloli 171
  • Bayan rushe zaben ciyamomin, Mai shari'a Oshomoah ya kuma dakatar da gwamnatin Ebonyi daga gudanar da wani sabon zabe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Babbar kotun tarayya da ke zama a Abakaliki, jihar Ebonyi, ta soke zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a watan Yuli 2024 tare da tsige ciyamomi 13 da kansiloli 171.

Alkalin kotun, Mai shari’a H.I.O. Oshomah, ya bayyana cewa hukumar zabe ta jihar Ebonyi (EBSIEC) ta gudanar da zabukan ne ba tare da bin ka’idojin dokar zabe ba, wanda hakan ya sa kotun ta soke zaben.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sun gano kuskuren kotu da ta ba da umarnin aurar da ƴan TikTok a Kano

Babbar kotun tarayya ta soke zaben kananan hukumomi da aka gudanar a Ebonyi.
Hoton kofar shiga cikin babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

Kotu ta soke zaben ciyamomi a Ebonyi

Kotun ta kuma hana gwamnati da EBSIEC sake gudanar da wani sabon zabe har sai an bi cikakkun tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan wanda ya shigar da kara na farko, Hamilton Ogbodo, ya ce hukuncin ya tabbatar da cewa dokar kasa ce ta yi nasara a kan rashin gaskiya da son zuciya.

“A yau kotu ta tabbatar da cewa zaben kananan hukumomi da aka yi a watan Yuli 2024 ba shi da inganci,” in ji Ogbodo.

Ya kara da cewa:

“Idan gwamnati da hukumar zabe suna son bin doka, su koma matsayin da doka ta tanada kuma su aiwatar da umarnin kotu yadda ya dace.”

Ogbodo ya ce hukuncin kotun ya bayyana a fili cewa babu wani gwamnati da ke sama da doka a Najeriya.

'Gwamnatin Ebonyi ta saba doka' – Lauya

A nasa bangaren, Mudi Erhenede, lauyan wanda ya shigar da kara na biyu, ya tuna cewa kotu ta taba soke zabukan ciyamomin jihar na 2022, amma gwamnati ta ki bin hukuncin.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

Ya ce duk da cewa gwamnatin jihar ta daukaka kara, kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin da Mai shari’a Fatun Riman ya yanke a wancan lokaci.

Erhenede ya zargi gwamnatin jihar da kin mutunta doka da kotu, yana cewa hakan ya zama alamar raini ga tsarin shari’a a kasar nan, inji rahoton Vanguard.

Lauyoyi sun zargi gwamnatin Ebonyi da bijirewa umarnin kotu kan zaben ciyamomin jihar.
Taswirar jihar Ebonyi da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Lauya ya yaba da hukuncin kotu

Erhenede ya yabawa sabon hukuncin da Mai shari’a Oshomah ya yanke kan zaben ciyamomi na 2024, yana mai cewa hakan zai dawo da gaskiya da mutuncin tsarin zabe a Ebonyi.

Ya kuma bukaci kotu ta fitar da cikakken kwafi na hukuncin a kan lokaci domin tabbatar da aiwatar da shi ba tare da an samu wani jinkiri ba.

Ya ce wannan hukunci darasi ne ga sauran jihohi da ke yin zaben ciyamomi ba bisa doka ba domin biyan wasu bukatu na siyasarsu.

Soke zaben ciyamomin Ebonyi a 2022

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, ko a shekarar 2022, babbar kotun tarayya ta soke zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi hanya 1 da APC za ta iya lashe zaben gwamna a jihar Oyo

A cewar Kotun, zaɓen kananan hukumomin da ya gudana ranar 30 ga watan Yuli, 2022, ya saɓa wa tanadin sabon kundin dokokin zaɓen 2022.

Alƙalin kotun, Mai shari'a Justice Rilman Fatun, ya yanke hukuncin cewa zaɓen ya saɓa wa tsarin demokaraɗiyya da tanadin doka, don haka ya soke shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com