Tsautsayi: Mawakin Hausa Ya Gamu da Ajali, Ya Rasu bayan Ya Ci Abinci a Jihar Bauchi
- Mawakin Hausa, John Zuya, ya rasa rayuwarsa bayan ya ci abinci da ake zargin yana dauke da guba da ya jawo masa matsala
- Rahotanni sun bayyana cewa mawakin, wanda aka fi sani da John Mai Molo ya mutu ne ranar Asabar da ta gaba a yankin Tafawa Balewa
- Abokinsa da suke waka tare, Emma Wakili ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbin mutuwar John Mai Molo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Shahararren mawakin gargajiya, John Zuya, wanda aka fi sani da John Mai Molo, ya rasu bayan cin abincin da ake zargin an saka masa guba a Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa mawakin wanda aka fi sani da John Mai Molo ya rasu a yankin Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, bayan wani lamari mai cike da ban tausayi.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana

Source: Facebook
The Cable ta tattaro cewa lamarin ya auku ne bayan John Mai Molo ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Legas a ranar 16 ga Oktoba, inda ya halarci wasu bukukuwa na gargajiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda mawakin gargajiya ya rasu a Bauchi
An ruwaito cewa bayan ya koma Bauchi, ya ci abinci, daga nan ya fara jin rashin lafiya mai tsanani har ta kai ga ya suma.
Daga nan ne aka garzaya da shi asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) amma likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu tun kafin a fara kula da shi.
Abokin aikinsa, Emma Wakili, ya wallafa a Facebook cewa John Zuya ya rasu da misalin karfe 7:00 na safe ranar Asabar, yana mai cewa ana gudanar da bincike kan musabbabin mutuwarsa.
Ya rubuta cewa:
“An tabbatar da mutuwar John Zuya da karfe 7:00 na safiyar Asabar. An kai gawarsa dakin ajiye gawa yayin da ake ci gaba da bincike.”
An fara bincike kan mutuwar John Mai Molo
Bugu da kari, Wakili ya bayyana bakin cikinsa game da rasa abokinsa, yana cewa John ya wuce ya kira shi da aboki kadai domin ya zama dan’uwansa.
“Daya daga cikin abubuwan da suka fi bani tsoro da ciwo a rayuwata shi ne rasuwar John Zuya. Ba kawai aboki ba ne, dan uwa ne.
"Muna da buri a rayuwa, mun tsara makoma, mun shirya gina gobenmu mai albarka, amma yanzu ya tafi,” in ji shi.
Ya kara da cewa mutuwarsa ta bar tambayoyi da yawa, yana mai jaddada cewa “Allah ba azzalumin kowa ba ne; gaskiya za ta fito fili kuma adalci zai tabbata."

Source: Facebook
John Mai Molo ya shahara a Arewacin Najeriya saboda gudunmawar da ya bayar wajen raya al’adun gargajiya da kuma wakokin nishaɗi da barkwanci a harshen Hausa.
Ya shahara musamman da wakokin “Abar Matasa” da “Chaskale”, wadanda ya rera tare da abokinsa Emma Wakili.
Babban 'dan kasuwa a Najeriya ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa fitaccen dan Kasuwa a Najeriya, Alhaji Ali Oladeinde Akinyele ya riga mu gidan gaskiya bayan ya sha fama da doguwar jinya.
Sanannen ɗan kasuwar, wanda ya kafa manyan kamfanoni AkinOcean Nigeria da Allison Foam ya rasu ranar Laraba 15 ga watan Oktobar 2025.
A lokacin rayuwarsa, Akinyele ya horar da matasa da dama a fannin kasuwanci, ciki har da wadanda suka zama manyan ‘yan kasuwa kamar shugaban BUA Group, Abdulsamad Rabiu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

