Trump Ya Kinkimo Babban Aiki, Ya Fara Rushe Wani Bangare na Fadar White House
- Donald Trump ya fara rushe wani bangare na gabashin fadar shugaban kasar Amurka don gina dakin taro
- Sabon dakin taron zai karbi baki kusan 1,000, yayin da aka ce zai lakume kimanin dala miliyan 250
- An gina 'East Wing' a 1942 lokacin Franklin Roosevelt, kuma rushe shi yanzu ya tayar da cece-kuce a kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka — A ranar Litinin, an ga ma’aikatan gini suna rushe wani bangare na 'East Wing' da ke cikin Fadar White House.
An ce Shugaba Donald Trump ne ya ba da umarnin rushe bangaren Gabashin fadar shugaban kasar Amurkan don gina dakin taro.

Source: Twitter
An fara rushe wani bangare na White House
Rahoton Reuters ya nuna cewa aikin gina sabon babban dakin taron da Shugaba Trump ke son yi zai lashe dala miliyan 250.

Kara karanta wannan
Rashawa: Kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasa hukuncin zaman gidan yari a Faransa
Tun ma kafin a fara aikin, Donald Trump ya shaida wa duniya cewa da kudin aljihunsu da na 'yan gudunmawa ne za a gina dakin taron.
An dai ga manyan injinan gine-gine suna lalata bangon ginin East Wing, bangaren da aka saba amfani da shi a matsayin ofishin uwargidar shugaban kasa, dakin kallo, da kuma kofar karbar bakuncin baki daga kasashen waje.
Wannan aiki, yana daya daga cikin canje-canjen gine-gine mafi girma da aka taba yi a fadar White House cikin shekaru masu yawa.
A watan Yuli, Trump ya bayyana cewa “kyakkyawan gini ne” wanda ba zai lalata tsarin asali na fadar ba.
“Zai zama mafi kyawun dakin taro”
Da yake jawabi ga ’yan wasan kwallo na jami’ar Louisiana State a cikin dakin 'East Room' a ranar Litinin, Trump ya tabbatar da cewa an fara aikin ginin a hukumance, yana mai cewa:
“A nan bayan mu ake aikin ginin. Kuna iya jin karar injina suna aiki — suna nan suna aiki sosai.”
Trump ya bayyana cewa sabon dakin zai iya karbar mutane kusan 999, kuma zai kasance da kayatattun fitilu, katafaren bango irin na Italiya, da da'irar hango husumiyar Washington.
Kafar watsa labarai ta CNN ta ruwaito Trump ya bayyana cewa:
“Sabon ginin yana dab da White House, amma ba zai shafi giinin na asali ba. Bayan an gama, zai zama mafi kyawun dakin taro a Amurka.”

Source: Twitter
Tarihin 'East Wing' na Fadar White House
An gina bangaren gabashin White House a shekarar 1942 lokacin mulkin shugaban kasa Franklin D. Roosevelt, a saman wani dakin tsaro da aka gina domin kariya ga shugaban kasa a lokacin yakin duniya na biyu.
Tun daga lokacin, ginin ya rika cunkushewa saboda yawan ma’aikata da baki, wanda hakan ke sa aka rika yin bukukuwa da taruka a cikin tanti a waje.
Masana tarihi sun nuna damuwa cewa wannan aikin da Trump ya tattago na iya lalata tsarin tarihi na fadar, duk da cewa Trump ya dage cewa aikin “yana girmama tarihin Amurka.”
An cire hoton Obama a White House
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an sauya hoton Barack Obama da wani sabon zane da ke nuna Donald Trump bayan yunƙurin kashe shi.
Zanen ya nuna lokacin da Trump ya ɗaga hannunsa bayan an harbe shi a kunne, a lokacin da yake yakin neman zaben shugaban kasa.
An ce za a maida hoton George W. Bush kusa da na mahaifinsa, aka matsar da na Obama zuwa bangon da aka saka hoton Bush.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

