Shettima Ya Mika Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa ga Wata Budurwa
- Kashim Shettima ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da cikakken niyyar tallafawa ilimin ‘ya’ya mata a fadin Najeriya
- Shettima ya karɓi tawagar PLAN International inda ya gayyaci wata budurwa mai suna Joy Ogah ta zama mataimakiyar shugaban kasa
- Bayan hawa kujerar na rana daya, Joy Ogah ta yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da ingantaccen ilimi da kariya ga dukkan ‘ya’ya mata
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da cikakken kudiri wajen inganta ilimin ‘ya’ya mata a Najeriya.
Shettima ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da tawagar PLAN International karkashin jagorancin Helen Mfonobong Idiong a ranar 21, Oktoba, 2025.

Source: Facebook
A sakon da Shettima ya wallafa a X, ya bai wa wata yarinya, Joy Ogah, damar zama mataimakiyar shugaban kasa na rana guda domin bayyana ra’ayinta kan batun ‘ya’ya mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin Shettima yayin ganawa da PLAIN
Shettima ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da hada kai da kungiyoyin ci gaban al’umma kamar PLAN International domin ciyar da harkar ilimin ‘ya’ya mata gaba.
Ya ce shirin ciyar da dalibai a makarantu yana daga cikin muhimman tsare-tsare da gwamnati ke ganin ya kamata a cigaba da shi domin inganta lafiyar yara da karatunsu.
Shettima ya kuma bayyana matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, a matsayin abin koyi na yadda mace za ta iya kaiwa ga manyan mukamai idan aka ba ta dama da tallafi.
Joy Ogah ta zama mataimakiyar shugaban kasa
Bayan jawabin Shettima, wata budurwa, Joy Ogah ta karbi kujerar mataimakin shugaban kasa inda ta nuna farin kan samun damar.
Ta bayyana cewa fiye da yara miliyan 10 ne ba su zuwa makaranta a Najeriya, kuma kashi 60 cikin 100 daga cikinsu mata ne.

Source: Facebook
Ogah ta yi kira ga gwamnati da masu tsara manufofi su dauki matakai na gaggawa wajen tabbatar da ilimi mai inganci da kariya ga ‘ya’ya mata.
Kiran Joy Ogah ga gwamnati da al’umma
A jawabinta, Ogah ta jaddada bukatar gwamnati ta tabbatar da tsaro a makarantu, tare da samar da kayan tsaftace jiki kyauta ga ‘ya’ya mata.
Ta kuma yi kira da a tabbatar da dokokin da ke kare ‘ya’ya mata daga cin zarafi da tauye hakki a Najeriya.
A cewarta:
“Lokacin da aka kare ‘ya’ya mata, zaman lafiya zai samu.”
A karshe, Mataimakin Shugaban Kasa ya tabbatar wa PLAN International cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da kasancewa abokiyar hulɗa wajen ciyar da harkar ilimin ‘ya’ya mata gaba.
Shettima zai kaddamar da NJFP 2.0
A wani rahoton, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima zai kaddamar da shirin NJFP 2.0 a ranar Laraba.
Bayan kammala zagayen farko, mataimakin shugaban kasar ya ce shirin zai taimaka wajen samar da ayyuka 20,000 a zagaye na biyu.
Bayanan da Legit Hausa ta samu sun tabbatar da cewa kungiyar tarayyar Turai (EU) na cikin masu tallafawa shirin NJFP 2.0.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


