Gwamnatin Gombe Ta Toshe Kofar Satan Yara, Ta Ceto 59
- Gwamnatin Gombe ta sanar da yadda ta samu nasarar ceto yara 59 daga hannun masu safarar mutane cikin watanni takwas
- Ta ce an cimma wannan nasara ne bayan haɗa duk tashoshin mota da ke jihar zuwa wuri guda, sannan aka zamanantar da shi
- Shugaban kamfanin motocin Gombe line na jihar, Dr. Sani Sabo ya bayyana cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya sayo sababbin motoci 80
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da cewa an ceto yara 59 da ake zargin masu safarar mutane ne suka yi yunkurin fitar da su daga jihar, cikin watanni takwas kacal.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta aiwatar da sabon tsarin sufuri da ya haɗa dukkanin tashoshin mota a jihar cikin wuri guda.

Source: Facebook
The Sun ta wallafa cewa Shugaban Gombe Line Transport Service, Dr. Sani Sabo, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gombe: An samu nasarar dakile satar yara
Daily Post ta wallafa cewa Dr. Sani Sani ya bayyana cewa wannan mataki ya taimaka sosai, domin ya sauƙaƙa wa hukumomin tsaro aikin sa ido da ɗaukar matakin gaggawa.
Ya ce:
“Muna aiki tare da ’yan sanda, hukumar NDLEA, NAPTIP da NSCDC, kuma cikin watanni takwas mun gano miyagun kwayoyi, makamai, da kuma ceto yara 59 daga hannun masu safarar mutane."
Ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne bayan mayar da dukkanin tashoshin mota zuwa babbar tashar mota ta Ibrahim Dankwambo.
Dr. Sani Sidi ya ce wannan tsarin yana sa duk wata tafiya ta kasance mai sauƙin bibiya, tare da hana tafiye-tafiya da su ka saba doka.
Gwamnatin Gombe ta saukaka sufuri
Baya ga batun tsaro, gwamnatin jihar ta zuba sababbin motoci 80, wanda hakan ya ƙara yawan motocin Gombe Line zuwa 92.

Kara karanta wannan
Gwamna ya bi sahun Peter Mbah ya koma jam'iyyar APC mai mulki? Gaskiya ta bayyana

Source: Facebook
Dr. Sabo ya ce wannan sauyi ya rage haɗurran hanya da kuma inganta aikin sufuri a birnin Gombe cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ya kara da cewa:
“Wannan sauyi yana nuna shugabancin Gwamna Inuwa Yahaya mai fifita bukatun jama’a. Ba kawai kudin shiga mu ke nema ba, muna kare rayuka ne.”
Ya kuma ja kunnen jama’a da su daina hawa motoci a wajen tashar gwamnati domin guje wa fadawa hannun masu aikata laifi.
An kai barawon yara kotu
A baya, kun ji cewa wata babbar kotun a jihar Kano ta bada umarnin a tura Ogugua Christopher da ake zargi, wanda ke da gidan marayu a Asaba, jihar Delta, zuwa gidan yari.
Ana tuhumar Christopher da wasu mutanen uku da safarar yara guda 15 daga Kano zuwa wasu jihohi a Kudancin kasar nan a tsakanin watan Yuni 2016 zuwa Disamba 2021.
Lauyan gwamnati ya shaidawa kotu cewa yayin zaman ranar Talata, ba a samu kawo sauran matan biyu - Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne duk da kokarin da su ka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
