Nnamdi Kanu: 'Yan Sanda Sun Yi Bayani kan Harbin Masu Zanga Zanga a Abuja

Nnamdi Kanu: 'Yan Sanda Sun Yi Bayani kan Harbin Masu Zanga Zanga a Abuja

  • Rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta karyata batun harba ashi kai tsaye a zanga-zangar #FreeNnamdiKanu da ya gudana a ranar Litinin
  • Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya ce an yi amfani da hayaki mai sa hawaye ne kawai domin tarwatsa jama'a
  • An kama masu zanga-zanga takwas a Abuja, yayin da wasu fasinjoji da su ke harkokinsu suka sha hayaki a tsakiyar birnin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) ta bayyana cewa ba ta taba amfani da harsashi kai tsaye ba a yayin zanga-zangar da aka gudanar a ranar Litinin.

'Dan gwagwarmaya kuma mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore ne ya jagoranci zanga-zangar #FreeNnamdiKanu a Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan gwamnoni 2 sun fita, gwamnan PDP ya kawo karshen jita jitar zai koma APC

Yan sanda sun musanta harbin masu zanga-zanga
Hoton Sufeton yan sandan kasa, Kayode Egbetokun Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Benjamin Hundeyin, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ya bayyana karyata cewa sun harbi jama'a da harsasai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun yi magana a kan zanga-zangar

The Channels Television ta wallafa cewa rundunar 'yan sanda ta ce jami’an ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye ne kawai don tarwatsa masu zanga-zangar.

Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa an dauki matakin amfani da hayakin ne saboda masu zanga-zanga sun yi yunkurin kutsawa yankin da wata kotu ta haramta shiga.

Yan sanda sun ce hayaki mai sa hawaye aka harba wa jama'a
Hoton Kayode Egbetokun da wasu jami'an yan sanda Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Hundeyin ya bayyana cewa:

“Zan iya tabbatar da cewa babu harbin harsashi ko guda daya da aka yi a yau (Litinin).”
“Wasu mutane da ba su saba jin sautin hayaki mai sa hawaye ba na iya dauka cewa harbin bindiga aka yi. Amma gaskiya ba a harba ko guda ba.”

Hundeyin ya ce jami’an rundunar sun fara da gargadi ga masu zanga-zangar, amma suka ki janye wa, suka ci gaba da matsowa zuwa wuraren da kotu ta hana shiga.

Kara karanta wannan

Yadda yan sanda suka dakume 'yan jaridan Faransa 2 a zanga zangar Nnamdi Kanu

Masu zanga-zanga sun fusata yan sanda

Kakakin 'yan sanda sun ce jami’an sun bi duk matakan aiki na doka kafin su yanke shawarar yin amfani da karfin da ya dace da halin da ake ciki.

Hundeyin ya ce:

“Mun fada cewa za mu aiwatar da umarnin kotu, kuma mun gargade su da su janye. Amma sun nace, suka ci gaba da matsowa."
“Mun bi ka’idojin aiki na rundunar yan sanda, kuma mun yi amfani da karfi kadan– wanda ya yi daidai da irin turjewar da muke fuskanta.”

Rahotanni sun nuna cewa an kama masu zanga-zanga takwas a ranar farko na gangamin da ke neman hukumomin kasar nan su saki Nnamdi Kanu.

Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, na hannun hukumar DSS tun bayan sake kama shi a watan Yunin 2021, kuma har yanzu yana fuskantar shari’a a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Yan sanda sun firgita masu zanga-zanga

A baya, kun ji cewa jagoran zanga‑zangar neman sako na Nnamdi Kanu, Omoyele Sowore, ya ce wani ɓangare na jami’an tsaro sun farmaki masu zanga‑zanga a babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutanen da suka fita neman na kansu a Zamfara

Ƙari ga haka, ya bayyana cewa an kama ɗan uwan Nnamdi Kanu da lauyansa, wanda hakan ya sa an firgita mutane a wurin duk da cewa ba su dauko batun da tashin hankali ba.

Sowore da tawagarsa sun gudanar da zanga zanga a birnin Abuja a kokarinsu na tursasawa gwamnatin tarayya ta saki Nnamdi Kanu, yayin da ake zarginsa da cin amanar kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng