Kusa a APC Ya Ba Shugaba Tinubu Shawara kan Yajin Aikin ASUU
- Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) na ci gaba da yajin aikin gargadi da ta shiga a fadin Najeriya
- Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya tsoma baki kan yajin aikin da kungiyar ASUU take yi
- Farfesa Haruna Yerima ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta shawo kan matsalar don kare kimar gwamnatinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC, Farfesa Haruna Yerima, ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yajin aikin kungiyar ASUU.
Farfesa Haruna Yerima ya bukaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta warware matsalolin da ke tsakaninsa da kungiyar ASUU domin kada lamarin ya zubar da mutuncin gwamnatinsa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki
ASUU ta shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu a makon da ya gabata saboda zargin cewa gwamnati ta kasa cika yarjejeniyar da ke tsakaninta da kungiyar.
Kungiyar ta bayyana cewa malaman jami’o’in Najeriya su ne mafi talauci a Afirka, inda suke karbar albashi kasa da takwarorinsu a kasashe kamar Zimbabwe, Ghana, da Uganda.
Wace shawara aka ba Bola Tinubu?
Farfesa Yerima wanda ya taba zama dan majalisar wakilai, ya shawarci Shugaba Tinubu da ya guji irin kura-kuran da suka jawo yajin aiki mai tsawo a zamanin tsofaffin shugabanni, wanda hakan ya jefa jami’o’in gwamnati cikin durkushewa.
“Shugaban kasa, kai mutum ne mai fahimtar gaskiya, kuma ka san halin da jami’o’inmu ke ciki, gine-gine sun lalace, tazara mai nisa tsakanin adadin dalibai da malamai, kayan aiki sun yi kadan. Waɗannan su ne abubuwan da ASUU ke fafutuka akai.”
- Farfesa Haruna Yerima

Kara karanta wannan
Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC
Ya kara da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa sun shafi malaman jami’a kai tsaye.
“Abin da farfesoshi ke samu a wata ba ya isa su biya bukatunsu na yau da kullum, daga kudin makaranta, zuwa kiwon lafiya da sauran bukatun yau da kullum."
- Farfesa Haruna Yerima

Source: Twitter
Farfesan ya ja hankalin Shugaba Tinubu cewa matasa, wadanda yawancinsu ke jami’o’i, sune ginshikin goyon bayansa, don haka bai kamata ya yi wasa da makomarsu ta hanyar bari a ci gaba yajin aikin ba.
“Kada ka maimaita kuskuren da tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari ya yi, wanda a mulkinsa aka yi yajin aikin ASUU mai tsawo wanda ya zama na biyu mafi tsawo a tarihin Najeriya."
"Ana iya magance wannan matsala gaba daya idan aka bi yarjejeniyoyin da suka dace. Kana da iko da karfin aiwatar da hakan."
"’Yan Najeriya suna da cikakken kwarin gwiwa cewa za ka iya kawo karshen wannan dadadden rikicin, kuma muna da tabbacin ba za ka ba su kunya ba ba."

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: 'Yan APC sun ja kunnen shugaban jam'iyyar kan tazarcen Tinubu a 2027
- Farfesa Haruna Yerima
NLC za ta sa kafar wando da gwamnati
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ta yi martani kan matakin gwamnatin tarayya na kin biyan malaman jami'an da suka shiga yajin aikin albashinsu.
NLC tare da kungiyoyin da ke karkashinta a bangaren ilmi na shirin daukar matakin ba albashi ba aiki.
Kungiyar NLC ta goyi bayan ASUU da kawayenta, inda ta shirya taya su yajin aikin idan aka gaza shawo kan matsalar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
