Kotu Ta Shiga tsakanin Uba da Ɗa kan Sayar da Gida a Kano
- Wata kotun shari’ar Musulunci a Kano ta saurari karar da wani Muhammad Shaddadu ya shigar gabanta
- Muhammad Shaddadu na zargin mahaifinsa ya cefanar masa da gida ba tare da sani ko izininsa ba a lokacin yana daure
- Ɗan nasa ya ce mahaifin ya taɓa tuhumarsa da hannu a kisan ɗan’uwansa kafin daga baya kotu ta wanke shi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke unguwar Danbare a jihar Kano saurari shari'ar da aka shigar a kan wani bawan Allah mai suna Malam Shaddadu.

Kara karanta wannan
Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC
Ɗan mutumin, Muhammad Shaddadu, ne ya kai ƙarar mahaifinsa zuwa kotu, inda ya bayyana cewa ubansa ya sayar masa da gidan da ya mallaka na tare da izini ba.

Source: Original
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Muhammad ya ce rikicin ya samo asali ne bayan mahaifinsa ya saya wa wasu ‘yan uwansa biyu Keke Napep.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: Yadda aka samu sabani tsakanin uba da 'da
A cewar Muhammad Shaddadu, wasu ɓata-gari sun kai wa ɗaya daga cikin ‘yan uwansa hari, inda suka kashe shi suka kuma kwashe baburinsa.
Muhammad ya ce sai mahaifinsu ya ɗora masa alhakin wannan harin, ya kai shi kotu, kuma aka tsare shi a gidan yari a lokacin da ake shari'ar.

Source: UGC
Sai dai daga bisani, kotu ta wanke Muhammad daga duk wata tuhuma, amma da ya koma gida, sai ya gano cewa mahaifinsa ya sayar da gidansa.
Ya ce yana zargin mahaifinsa da sayar da gidan bisa zargin cewa ba zai samu nasarar fito wa daga gidan yari da aka tura shi kan zargin kashe dan uwansa ba.
Kotu ta nemi a sasanta uba da dansa
Lokacin da aka karanta masa tuhumar a gaban kotu, Malam Shaddadu ya musanta zargin, yana mai cewa bai aikata laifin komai ba, kamar yadda ake zargin ya yi.
Alƙalin kotun, Malam Munzali Idris Gwadabe, ya bayyana cewa lamarin ya shafi dangantaka ce ta uba da ɗa, wanda ya kamata a bi ta hanyar fahimtar juna ba takaddama ba.
Saboda haka, ya miƙa shari’ar zuwa kotun sasanci, domin a yi ƙoƙarin samun sulhu da maslaha tsakanin ɓangarorin biyu maimakon ci gaba da shari’a a kotu a kan batun.

Kara karanta wannan
Hadimin gwamnan Kano ya janye korafi a kan dan jarida, yan sanda sun saki Dan Uwa Rano
Uba da ɗa sun gurfana a gaban kotu
A baya, mun wallafa cewa wata kotun majistare a garin Ile-Ife, jihar Osun, ta gurfanar da wani Pius Miller, mai shekara kusan 52 bisa zargin aikata sata a harabar asibiti a jihar.
An maka shi a gaban kotun tare da dansa mai suna Israel, ɗan shekara 17, bisa zargin satar waya ta kamfanin sadarwa, laifin da ya saba da dokokin jihar da Najeriya.
Dan sanda mai gabatar da kara, Sunday Osanyintuyi, ya shaida wa kotu cewa lamarin ya faru ne a ranar 30 ga Yuli, 2025 lokacin da wadannan ake zargin suka yi yunkurin satar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
