‘Da da Uba Sun gurfana a gaban Kotu bisa laifin sata

‘Da da Uba Sun gurfana a gaban Kotu bisa laifin sata

- Tabarbarewar Tarbiyya ta sanya wani Uba da yaronsa hada baki don yin sata

- Amma sai dai bayan satar kayan da darajar su ta kai Naira 11,700 asiri ya tonu

- Har an gurfanar da su gaban alkali don tuhuma

A jiya ne wani Uba mai suna Pius Miller mai kimanin shekaru 52 tare da dansa Israel dan shekara 17 suka gurfana gaban wata kotun majistire dake garin Ile-Ife a jihar Osun, bisa zarginsu da satar wata wayar kamfanin sadarwa wacce ta kai darajar Naira 11,700.

‘Da da Uba Sun gurfana a gaban Kotu bisa laifin sata
‘Da da Uba Sun gurfana a gaban Kotu bisa laifin sata

‘Dan sanda mai gabatar da kara Sunday Osanyintuyi ya bayyanawa kotun cewa a ranar 30 ga watan Yuli ne, wadanda ake zargin suka sace kebIl din wayar sadarwar dake harabar Asibitin Koyarwa na jami'ar Obafemi Awolowo.

KU KARANTA: Tirkashi: Wani mutum yayi kisan kai a wurin jana’izar surikarsa

Sunday Osanyintuyi ya kuma ce laifin ya saba da sashi na 383,390 (9) da kuma sashi na 516 na kundin manyan laifuffuka da kuma dokokin jihar Osun na Shekarar 2002.

Lauyan wadanda ake kara Mista Ben Adirieje, ya bukaci kotun da ta bayar da belin wadanda ake tuhumar domin ba zasu tsere ba.

A karshe alkalin kotun majistiren mai shari’a Ishola Omisade ya bayar da belinsu akan kudi Naira 100,000 tare da gabatar da wanda zai tsaya musu, sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Satumba domin cigaba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng