ADC Ta Gargadi Gwamnatin Tinubu kan Batun Yunkurin Juyin Mulki a Najeriya

ADC Ta Gargadi Gwamnatin Tinubu kan Batun Yunkurin Juyin Mulki a Najeriya

  • Jam'iyyar ADC ta tsoma baki kan batun yunkurin yin juyin mulki ga Mai girma Bola Tinubu da ake ta magana a kai
  • Kakakin ADC ya nuna damuwa kan yadda gwamnati take fitar da bayanai masu cin karo da juna kan batun yunkurin juyin mulki
  • Mallam Bolaji Abdullahi ya bukaci kada a yi amfani da zargin juyin mulkin wajen danne 'yan adawa a Najeriya

Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta gargaɗi gwamnatin tarayya kan batun da aka yadawa na yunkurin juyin mullki a Najeriya.

Jam'iyyar ADC ta bukaci gwamnati da kada ta yi amfani da batun yunkurin juyin mulki a matsayin hujja don tsoratar da ’yan adawa ko kuma yin leken asiri ba bisa ka’ida ba kan masu sukar gwamnati.

ADC ta ja kunnen Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran ADC na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Lokacin da aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Obasanjo a mulkin farar hula

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ADC ta ce kan yunkurin juyin mulki?

Jam'iyyar ADC ta ce tana daukar duk wani barazana ga tsarin dimokuradiyya da muhimmanci, amma ba za ta amince da amfani da hakan wajen danne ’yancin magana ko neman amfani da tsaro a matsayin makamin siyasa ba.

"Ko da yake muna adawa da duk wani yunkuri na rugujewar kundin tsarin mulkin Najeriya, muna da damuwa game da yadda za a iya amfani da wannan zargi wajen yin farautar siyasa, danne ’yan adawa, ko karkatar da hankalin jama’a."

- Mallam Bolaji Abdullahi

Jam’iyyar ta bayyana cewa tana bin diddigin labaran da ke cewa an kama wasu jami’an sojoji da ake zargi da hannu a juyin mulki, da kuma rahotannin cewa ana binciken tsohon gwamnan wata jiha daga Kudu bisa zargin taimakawa wadanda ake zargi.

ADC ta nuna damuwa da yadda hukumomin gwamnati ke fitar da bayanai masu karo da juna, musamman bayan da hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta musanta cewa ba ta taba ambaton wani yunkurin juyin mulki duk da yawan rahotannin da aka fitar ba.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: ACF da Afenifere sun aika sako ga sojojin Najeriya

“Wannan rashin daidaituwa yana tayar da hankali, domin yana iya nuna cewa labarin juyin mulkin an kirkire shi ne don dalilan siyasa."

- Mallam Bolaji Abdullahi

Jam'iyyar ADC ta ja kunnen gwamnatin tarayya
Kakakin ADC na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

ADC ta soki gwamnatin tarayya

Jam’iyyar ta kuma soki gwamnatin tarayya saboda rashin fito da cikakken bayani kan lamarin, tana mai cewa shiru daga bangaren gwamnati ya ba labarin damar yaduwa tare da haifar da shakku a zukatan ’yan kasa.

ADC ta kara da cewa gwamnatin na iya amfani da labarin juyin mulkin a matsayin dabara don karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin rashin kyakkyawan mulki da neman tausayi daga al’umma.

Ta kara da cewa akwai yiwuwar gwamnati ta yi amfani da rahotannin da ke nuna yatsa ga wasu 'yan siyasa, don kai hari kan ’yan adawa ta hanyar yunkurin danne su.

Uba Sani ya yi wa Tinubu albishir

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi wa Mai girma Bola Tinubu albishir kan zaben 2027.

Gwamna Uba Sani ya gayawa Shugaba Tinubu cewa jam'iyyar APC za ta samu kaso 95% na kuri'un da za a kada a jihar.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin juyin mulki har Tinubu ya soke bikin ranar 'yanci? An samu bayanai

Hakazalika ya bayyana cewa babu sauran wata adawa a Kaduna domin duk son koma jam'iyya mai mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng