'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mutanen da Suka Fita Neman Na Kansu a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mutanen da Suka Fita Neman Na Kansu a Zamfara

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika kan mutanen da suka fita neman na sanyawa a bakin salati a jihar Zamfara
  • Miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mahauta da dillalan dabbobi lokacin da suke kan hanyar dawowa daga kasuwa
  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta koka kan yadda mutane ba su yin gaggawar sanar da su idan irin wadannan al'amuran sun auku

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Wasu ’yan bindiga sun sace wasu mahauta da dillalan dabbobi guda shida a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun sace mutanen ne yayin da suke dawowa daga kasuwar Magajin Maitarko da ke kusa da dajin Dogon Santsi a karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar The Guardian ta kawo rahoto cewa wani daga cikin dan uwan wadanda abin ya shafa, Isyaku Umar, ya tabbatar mata da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Yadda yan sanda suka dakume 'yan jaridan Faransa 2 a zanga zangar Nnamdi Kanu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindiga suka sace mutane a Zamfara

Isyaku Umar ya bayyana cewa ’yan bindigan sun tare hanyar Gusau–Dansadau da yammacin ranar Juma’a.

"Yan bindigan sun harbi daya daga cikinsu, kuma yana cikin mawuyacin hali. Sun kira ta wayar daya daga cikin wadanda suka sace.”

- Isyaku Umar

Isyaku Umar ya kara da cewa, ’yan bindigar suna neman kudin fansa na Naira miliyan biyu don sako mutumin da suka ji masa rauni, amma ba su ce komai ba game da sauran mutum biyar din.

"Sun gargade mu cewa idan muka yi jinkiri wajen kawo kudin fansa, za su kashe shi saboda ba za su iya kula da rauninsa ba."
“Dan uwanmu wanda aka sace yana rokon mu sayar da gidansa domin mu biya kudin da ake nema, yanzu haka muna kokarin sayar da shi don a sake shi daga hannunsu."

- Isyaku Umar

Da aka tuntubi shugaban masu sayar da dabbobi a jihar, Malam Aminu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutane hudu daga cikin wadanda aka sace ’yan kungiyar su ne, labarin ya zo a rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun hallaka kwamandan bataliyar sojojin Najeriya da wasu jami'ai

'Yan sanda ba su da labari kan harin

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana cewa har yanzu ba su samu rahoton lamarin a hukumance ba.

Ya shawarci jama’a su rika sanar da irin wadannan abubuwa ga ofishin ’yan sanda mafi kusa don gaggawar daukar matakin da ya dace.

"Wasu mutanen ba sa kawo rahoton abubuwa irin wannan gare mu. Muna da tsare-tsare na musamman domin ceto wadanda aka sace."
"Sau da dama ana kawo mana bayanai bayan mutane sun kasa da kansu, kuma muna samun nasara wajen ceto su.”

- DSP Yazid Abubakar

An cafke hatsabiban 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasara kan wasu miyagun 'yan bindiga a jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Jami'an tsaron sun samu nasarar cafke manyan hatsabiban ‘yan bindigabiyu tare da masu daukar nauyinsu bayan wani samame da suka kai a wasu kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: 'Yan bindiga da makiyaya sun mamaye gari guda a Benue

Hakazalika, sun samu nasarar kwato makamai daga hannun miyagun masu tayar da kayar bayan a cikin al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng