Ana Zancen Kanu, Gwamna Soludo Ya Magantu kan Neman Raba Najeriya

Ana Zancen Kanu, Gwamna Soludo Ya Magantu kan Neman Raba Najeriya

  • Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya ce cigaban Igbo yana cikin hadin kan Najeriya, ba raba kasa ba
  • Soludo ya bayyana cewa ya goyi bayan tattaunawa cikin lumana amma ba ra’ayin ballewa a Najeriya da IPOB ke so ba
  • Ya ce dokar zaman gida ta ranar Litinin da kungiyar IPOB ta kawo ta daina tasiri saboda tsaro ya inganta a jihar Anambra

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


Jihar Anambra – Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya nesanta kansa daga masu neman ballewa daga Najeriya.

A cewarsa, ra’ayin raba kasa ba zai kawo wa yankin Kudu maso Gabas ci gaba ba, illa ya kara rarrabuwar kawuna da durkusar da tattalin arziki.

Gwamnan jihar Anambra
Gwamnan Anambra, Charles Soludo. Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Source: Facebook

Soludo ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels Television a ranar Lahadi, inda ya yi bayani kan matsayinsa game da al’amuran IPOB da zanga-zangar neman ‘yancin kai.

Kara karanta wannan

'Yar ƙwaya ce fa yanzu': Sanata ya ƙaryata zargin cin zarafin matarsa a gidan aure

Soludo: 'Cigaban Igbo yana Najeriya'

Soludo ya bayyana cewa yana goyon bayan tattaunawa cikin lumana da zanga-zangar da ba ta da tashin hankali, amma ba ya tare da ra’ayin ballewa da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ke nema.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta wallafa cewa ya ce:

“Mun bayyana a fili cewa, idan mutum yana zanga-zanga ne amma yana kashe ’yan uwansa da sunan zaman gida, to yana cutar da kansa.”

Gwamnan ya kara da cewa dokar zaman gida ta ranar Litinin ta ragu sosai a jihar Anambra, saboda tsaro da wayar da kai da gwamnati ta yi.

“Ba na goyon bayan zaman gida” – Soludo

Soludo ya bayyana cewa kowa da kowa da ke zama a gida yanzu yana yin hakan ne da yardarsa, ba saboda tsoro ba, domin a cewarsa tsaro ya tabbata a ko’ina cikin jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa kungiyar IPOB da kanta ta sha bayyana cewa ba ta goyon bayan zaman gida, tana zargin wasu ‘yan ta’adda ne suka yi amfani da shi wajen tada fitina.

Kara karanta wannan

MCAN: 'Yan NYSC Musulmi sun yi taron Arewa maso Gabas a Gombe

“Ina gode wa IPOB saboda bayyana wannan matsayi,”

Inji Soludo

Maganar Soludo kan fafutukar Biyafara

Yayin da yake jaddada mutuntakar ra’ayi da ’yancin zanga-zanga, Soludo ya ce nasa aikin shi ne gudanar da gwamnati ba shiga fafutuka ba.

“Masu fafutuka suna da aikinsu, ni kuma aiki na shi ne in yi mulki,”

In ji shi.

Ya kara da cewa ya bukaci shugabannin yankin Kudu maso Gabas da su tattauna da Nnamdi Kanu idan aka sako domin makomar yankin ba ta hannun mutum guda.

Shugaban IPOB, Kanu
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu a kotu. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

Gwamnan ya ce:

“Na ce a gayyace shi ya zauna da kowa da kowa,”

Masu zanga zangar Kanu sun gudu

A wani rahoton, kun ji cewa da safiyar yau Litinin ne masu zanga-zangar neman a saki shugaban kungiyar 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu.

Masu zanga zangar sun hadu da fushin jami'an tsaro yayin da suka fito suna tafiya a wasu yankunan Abuja.

Jagoran zanga zangar, Omoyele Sowore ya bukaci kada jami'an tsaro su harbe su da harsashi ko borkonon tsohuwa kafin rugawa da gudu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng