Ana Binciken Tsohon Gwamna kan Zargin Hannu a Shirin Yi wa Tinubu Juyin Mulki
- An ce tsohon gwamna daga Kudu na karkashin bincike saboda zargin hulɗa da wasu jami’an soji da ake zargi da yunkurin juyin mulki
- Majiyoyi sun ce ana zargin tsohon gwamnan da taimakawa da kudi wajen shirin juyin mulkin da aka ce za a yi ranar 25 ga Oktoba 2025
- A baya dai hedikwatar tsaron kasa ta musanta jita-jitar cewa an soke bikin cikar Najeriya shekaru 65 saboda zargin yunkurin juyin mulki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wasu majiyoyi sun ce tsohon gwamna daga Kudancin Najeriya na karkashin bincike bisa zargin cewa yana da hannu a yunkurin juyin mulki da wasu jami’an soji suka yi shirin yi.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama wasu hafsoshi 16 na rundunar soji da ake zargin suna da hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na daga cikin mutanen da ake zargin sun tallafa da kudi wajen shirin, wanda ake cewa an tsara za a gudanar da shi ranar 25 ga Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana cewa binciken yana karkashin kulawar Hukumar Leken Asirin Soji ta kasa (DIA), tare da wakilai daga sassan rundunonin soja uku.
Wata majiya ta tabbatar da cewa akwai hadin gwiwar wasu fararen hula a cikin lamarin, ciki har da tsohon gwamna wanda kafin shiga siyasa ya taba aiki a bangaren man fetur.
Juyin mulki: Ana binciken tsohon gwamna
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan yadda tsohon gwamnan ya yi hulɗa da jami’an da ake tsare da su.
A cewar majiyar, idan bincike ya tabbatar da alaƙa tsakaninsa da jami’an da ake zargi, za a gayyace shi domin amsa tambayoyi.
Rahotanni sun ce hafsoshin da ake bincike sun hada da wani Birgediya-Janar daga Jihar Neja, da wani Kanal daga Nasarawa.
Aminiya ta ce mahaifin Kanal din yana rike da sarauta a jihar, kana kuma ɗan uwan tsohon gwamna Umaru Tanko Al-Makura ne.

Source: Facebook
A Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, iyalan Al-Makura sun bayyana damuwa kan halin da ɗan uwansu yake ciki.
Wani daga cikin dangin sojan ya tabbatar da cewa matarsa da sauran iyalan suna cikin tashin hankali.
Ana cigaba da bincike kan ‘yan siyasa
Wata majiya ta bayyana cewa, baya ga tsohon gwamnan, ana sa ido kan wasu ‘yan siyasa da ake zargin suna da hannu ko masaniya game da shirin juyin mulkin.
Majiyar ta ce an kama karin wasu jami’an soji domin amsa tambayoyi kan irin hulɗar su da wadanda ake zargi tun farko.
An bayyana cewa kwamitin binciken ya kunshi manyan hafsoshin soja karkashin jagorancin wani Manjo Janar.
DHQ ta musanta jita-jita kan juyin mulki
A wani rahoton, kun ji cewa hedikwatar tsaron kasa (DHQ) ta ce cewa an soke shagulgulan bikin cikar Najeriya shekaru 65 saboda zargin juyin mulki ba gaskiya ba ne.
Kakakin hukumar, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan fara jita jitar.

Kara karanta wannan
An yi yunkurin juyin mulki har Tinubu ya soke bikin ranar 'yanci? An samu bayanai
Sanarwar ta ce rahoton wasu kafafen labarai da ke danganta kama hafsoshin soja 16 da zargin juyin mulki karya ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

