Ana Jita Jitar Juyin Mulki, an Gargadi Masu Zanga Zanga Kusantar Fadar Tinubu
- Rundunar ‘yan sanda ta yi gargadi mai tsanani ga masu shirin gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya, Abuja
- Yan sanda sun yi gargadi ga masu son a saki Nnamdi Kanu da su guji Aso Rock da kewaye saboda umarnin kotu
- Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin ya ce kotun tarayya ta hana duk wata zanga-zanga a kusa da fadar shugaban kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi gargadi ga masu shirin zanga-zanga a birnin tarayyar Najeriya za ke Abuja.
Rundunar ta yi gargadin ne ga masu neman sakin Mazi Nnamdi Kanu da ake zargin ta'addanci da cin amanar kasa.

Source: Facebook
Abin yan sanda suka ce nan shirin zanga-zanga
A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a Facebook, ta bukaci masu zanga-zangar da su guji Aso Rock da yankunanta baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Dakarun soji sun fafata da ƴan bindiga, an gano ƴan China da aka yi garkuwa da su
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya fitar daga birnin Abuja.
Hundeyin ya ce gargadin ya biyo bayan wata umarnin kotu da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar a ranar 17 ga Oktoba, 2025, a shari’ar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da Omoyele Sowore da wasu huɗu.
Kotun ta hana kowace kungiya ko mutum yin zanga-zanga a kusa da fadar shugaban ƙasa da sauran wuraren gwamnati.
A cewar sanarwar, wuraren da aka hana sun haɗa da Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Hedikwatar ‘Yan Sanda, Kotun Daukaka Kara, Eagle Square da hanyar Shehu Shagari.

Source: Facebook
An ja kunnen masu zanga-zanga a Abuja
Rundunar ta gargadi masu niyyar yin zanga-zanga da kungiyoyi da su guji waɗannan wurare domin kauce wa rikici da cunkoson jama’a.
Hundeyin ya ce rundunar za ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da kiyaye kwanciyar hankali a birnin tarayya.
Ya ce duk wanda ya yi amfani da zanga-zanga wajen haddasa tashin hankali, daukar makami ko barnar dukiya, za a cafke shi kuma a gurfanar da shi gaban kotu.
Ya ƙara da cewa, za a bi diddigin duk wanda ke tayar da hankali ta kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da hujjojin domin gurfanar da su bisa doka.
A cewarsa, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya umurci kwamishinan ‘yan sanda na Abuja da sauran hukumomin tsaro da su tabbatar da bin umarnin kotu da tsauraran matakan tsaro.
Ya kuma shawarci masu zanga-zanga su nemi hanyoyin shari’a wajen bayyana korafinsu maimakon hawa tituna, domin a kiyaye zaman lafiya da tsaron jama’a.
Rundunar tsaro ta ƙaryata jita-jitar juyin mulki
Kun ji cewa sojojin Najeriya sun yi karin haske kan yada cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya.
Rundunar ta kuma yi magana kan cewa har an kama wasu jami'an sojoji 16 da ake zarginsu da hannu a juyin mulki.
Hedikwatar Tsaron Ƙasa ta bayyana cewa labarin da ya danganta soke bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin kai da juyin mulki ba gaskiya ba ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
