Dangote Ya Ba 'Yan Najeriya Mafita kan Hanyar Samun Ayyukan Yi
- Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ba 'yan Najeriya shawara kan hanyar samar da ayyukan yi
- Aliko Dangote ya nuna cewa za a iya samar da ayyukan yi a kasar nan idan 'yan Najeriya suka rika sayen kayayyakin da aka kera a gida maimakon na waje
- Hamshakin attajirin ya bukaci 'yan Najeriya da su rika bada fifiko wajen sayen abubuwan da ake kera a kasar nan domin bunkasa tattalin arziki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shahararren attajirin Najeriya kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ba 'yan Najeriya shawara.
Aliko Dangote ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rika sayen kayayyakin da aka samarwa a cikin kasar nan domin bunkasa tattalin arzikin kasa.

Source: Getty Images
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa Dangote ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar, yayin da aka zagaya da manema labarai zuwa matatar man Dangote.

Kara karanta wannan
Minista ya tafi kasar waje, ya je duba jiragen yakin sojojin Najeriya da ake kerawa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zagaya da manema labaran ne karkashin jagorancin Reno Omokri, tsohon mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara, kuma mai yada shirin “GrowNairaBuyNaija”.
Wace shawara Dangote ya ba 'yan Najeriya?
Dangote ya ce duk ’yan Najeriya suna da alhakin hadin kai wajen gina kasa ta hanyar tallafawa kayayyakin da aka kera a gida.
Ya kara da cewa hakan ne mafita ta hakika idan ana son Najeriya ta bunkasa ta kai matakin kasashe masu ci gaba, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da labarin.
“Ina so na karfafa gwiwar ’yan Najeriya su rika sayen abin da aka kera a Najeriya. Idan ka sayi abin da aka kera a Najeriya, kana taimakawa wajen samar da ayyukan yi."
“Hanya daya tilo da za mu kara karfin kasa ita ce mu rika tallafa wa junanmu, mu rika sayen kayayyakin gida, domin hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma wadatar jama’a.”

Kara karanta wannan
Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema
- Aliko Dangote
An yabawa matatar Dangote
A nasa jawabin, Reno Omokri ya bayyana matatar man Dangote a matsayin muhimmiyar masana’anta wanda ke da ikon sauya tattalin arzikin Najeriya gaba daya.

Source: Facebook
“Matatar man Dangote ba ta daidai da yau ba ce ta gaba da yau ce, ita ce makomar Najeriya."
- Reno Omokri
Ya bayyana cewa tun bayan da matatar ta fara aiki shekara daya da ta gabata, fiye da jiragen ruwa 650 sun tashi daga tashar jiragen ruwa ta Dangote.
Ya ce kashi 60% na kayayyakin da ake fitarwa sun nufi Amurka, sauran kuma zuwa kasashen Brazil, Argentina da wasu kasashe.
An yi yunkurin lalata matatar Dangote
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar ta bayyana kalubalen da ta fuskanta tun lokacin da ta fara aiki a Najeriya.
Mataimakin shugaban kamfanin mai kula da sashen man fetur da iskar gas, Devakumar Edwin, ya bayyana cewa matatar ta fuskanci yunkurin lalata kayan aiki har sau 22.
Devakumar Edwin ya bayyana cewa duk da wadannan hare-haren, tsarin tsaro na zamani da masana’antar ke amfani da shi ya taimaka wajen dakile duk wani yunkuri na lalata kayayyakin aiki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
