MCAN: 'Yan NYSC Musulmi Sun Yi Taron Arewa Maso Gabas a Gombe
- Kungiyar masu hidimar NYSC Musulmi (MCAN) ta gudanar da babban taron Arewa maso Gabas a jami’ar jihar Gombe
- Legit ta gano cewa taron ya gudana a ranakun 18 da 19 ga Oktoban 2025 tare da halartar baki daga jihohin yankin baki daya
- An nada sababbin shugabannin MCAN na Arewa maso Gabas domin ci gaba da tafiyar da ayyukan kungiyar a ranar Lahadi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Kungiyar masu hidimar NYSC Musulmi (MCAN) ta gudanar da babban taronta na Arewa maso Gabas a jami’ar jihar Gombe, a ranakun 18 da 19 ga Oktoba, 2025.
Bayan Gombe mai masaukin baki, taron ya samu halartar wakilai daga jihohin Taraba, Adamawa, Bauchi, Yobe da Maiduguri.

Source: Original
Masana a fannoni daban-daban sun gabatar da jawabai kan yadda matasa za su iya zama masu dogaro da kai da kuma taka rawar gani a karni na 21.

Kara karanta wannan
Ta tabbata, sojojin Najeriya sun kama hatsabibin ɗan ta'adda da aka jima ana nema
Jawabin shugaban MCAN na kasa
Shugaban MCAN, Abdumalik Mahmud Adam, ya bayyana cewa babban burin kungiyar shi ne gina matasa musulmai masu tsantsar imani, basira da kishin kasa.
A sakon da MCAN ta wallafa a Facebook, shugaban ya ce shekara daya da suke a NYSC dama ce ga matasa ta kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’umma.
Shugaban ya kuma jaddada cewa makomar al’umma tana hannun jagorori masu hangen nesa da hadin kai.

Source: Original
Shugaban ya yi godiya da jami'ar Gombe, FCE (T) Gombe, 'yan kwamitin shura, NYSC, 'yan uwa da abokan arziki da suka taimaka wajen tabbatar da nasarar taron.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin Gombe da masarautar jihar da su samar wa MCAN motar bas ta zirga zirga kasancewar 'dansu ne ke jagorantar kungiyar a matakin kasa.
Takardu da aka gabatar a taron MCAN
Masana a fannoni da dama sun gabatar da makaloli domin nuna wa matasa hanyar zama masu dogaro da kai a zamanance.
An yi bayani kan hanyoyin samar da sana'o'i, bunkasa su a fannonin noma, kasuwanci da sauransu yayin taron.
Bugu da kari, daya daga cikin wadanda suka gabatar da takardu ta yi bayani kan yadda matan aure za su zama masu dogaro da kai tare da kiyaye hakkokin da ke kansu.
Shugabannin MCAN a Arewa maso Gabas
A yayin taron, an nada sababbin shugabannin MCAN na Arewa maso Gabas wadanda za su jagoranci ayyukan kungiyar a yankin.
Sababbin shugabannin sun hada da:
- Salisu Muhammad — Amir
- Jibrin Idris — Mataimakin Amir
- Zaliha Ishaq Baffah — Amira
- Abdullahi Adamu — Sakatare
- Ahmed Sagir Shehu — Mataimakin sakatare
- Mansur Haruna — Shugaban da’awa
- Alabi Abdulhafeez — Shugaban kasuwanci da kula da kayan kungiya
- Yasir Usman — Ma’aji
- Dahiru Yahaya Umar — Jami’in hulda da jama’a
- Abdulganiyyu Muhammad — Sakataren tsare-tsare
Jawabin mai martaba Sarkin Gombe
Taron ya samu halartar mai martaba Sarkin Gombe da Sarkin Yamma, Alhaji Shehu Baba Manu ya wakilta.
Alhaji Shehu Baba Manu ya sanar da cewa mai martaba Sarkin Gombe yana yi wa kungiyar MCAN fatan alheri.
Ya yi kira ga matasan su zama masu juriya kada su ji tsoron tunkarar abubuwan da suka saka a gaba a rayuwarsu.
Masu takardun bogi na shiga NYSC
A wani rahoton, kun ji cewa masu karatu a jami'o'in Kotono da Najeriya ta haramta karatu a can sun fito da dabarar shiga NYSC.
Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa daliban da suka yi karatu a Kotono na amfani da wasu kwalejojin fasaha wajen samun takardun bogi.
An yi kira ga ma'aikatar ilimi ta kasa da ta dauki matakin gaggawa wajen hana amfani da takardun bogi wajen shiga hidimar kasa.
Asali: Legit.ng

