An Nemi Tayar da Gobara a Matatar Dangote da Wasu Matsaloli Sama da 20

An Nemi Tayar da Gobara a Matatar Dangote da Wasu Matsaloli Sama da 20

  • Matatar Dangote ta bayyana cewa ta fuskanci yunkurin lalata mata kayan aiki har sau 22 tun daga lokacin da ta fara aiki
  • Mataimakin shugaban kamfanin, Devakumar Edwin, ya ce hare-haren sun nemi hana aikin matatar tafiya yadda ya kamata
  • Dangote ya ce sake fasalin masana’antar bai da nasaba da kungiyar ma'aikatan mai ta PENGASSAN da ta yi yajin aiki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


Jihar Legas – Matatar Dangote ta bayyana cewa masana’antar ta fuskanci yunkurin lalata kayan aiki sau 22 tun bayan fara aikin ta.

Mataimakin shugaban kamfanin mai kula da sashen man fetur da iskar gas, Devakumar Edwin, ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai.

Alhaji Aliko Dangote
Dangote da wani sashe na matatar shi. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa Edwin ya ce duk da wadannan hare-haren, tsarin tsaro na zamani da masana’antar ke amfani da shi ya taimaka wajen dakile duk wani yunkuri na lalata kayayyakin aiki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi karin haske kan bukatar dawo da zaben 2027 zuwa 2026

Matsaloli da Dangote ya samu a matata

Edwin ya bayyana cewa wasu daga cikin hare-haren sun hada da yunkurin cinna wuta ko bude bawul domin lalata kayayyaki, amma an gano su da wuri.

Ya ce:

“Mun rubuta bayanan dukkan hare-haren, tare da kwanan wata da wuraren da abin ya faru. Tsarin kariya na masana’antar yana gano duk wata matsala cikin kankanin lokaci.”

Ya kara da cewa duk da jita-jitar da ake yadawa, masana’antar ba ta fuskantar matsalar aiki ko karancin mai kamar yadda ake ikirari a wasu kafafe.

Akwai man fetur a matatar Dangote

Edwin ya bayyana cewa masana’antar tana da lita miliyan 312 na man fetur a ma’ajiyar ta, baya ga man da ake tacewa kullum.

Matatar Aliko Dangote
Marigayi Buhari a matatar Dangote. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Getty Images

Ya ce man ya isa ya biya bukatun Najeriya na fetur, dizal da man jirgin sama, tare da damar fitar da kusan rabin kayayyakin zuwa kasashen waje.

Edwin ya kara da cewa:

“Da farko sun ce masana’antar ba za ta kammala ba, daga bisani sun ce ba za ta fara aiki ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta jero abubuwan da suka jawo karyewar farashin abinci warwas

"Yanzu kuma suna yada labaran karya cewa tana da matsaloli, amma babu gaskiya a cikinsu.”

Reno Omokri ya yabi matatar Dangote

A yayin ziyararsa matatar, Reno Omokri ya ce ganin irin girman aikin ya tabbatar masa cewa masana’antar na taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Ya bayyana cewa sama da jiragen ruwa 650 ne suka riga suka dauki kayayyakin mai daga matatar Dangote cikin kasa da shekara guda.

This Day ta wallafa cewa Omokri ya ce hakan nasara ce babba da ta kara karfin tattalin arzikin kasa baki daya.

Dalilin tashin kudin mai a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa an nuna damuwa kan karuwar kudin litar man fetur a wasu jihohin Najeriya.

Bayanai da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa wasu 'yan kasuwa sun alakanta karin kudin da rashin samun mai sosai a matatar Dangote.

Wasu masu gidajen mai sun bayyana cewa manyan dilolin mai sun kara kudin lita bayan da Dangote ya daina sayar da mai na dan lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng