Rigima Ta Kunno Kai, an Roki Gwamna Ya Tsige Sarki da Aka Tura Gidan Yari

Rigima Ta Kunno Kai, an Roki Gwamna Ya Tsige Sarki da Aka Tura Gidan Yari

  • Gidajen sarauta sun fara gajiya bayan yankewa Sarkin garin hukunci dauri a gidan yarin Amurka
    Masarautar da ke Aribile da Fagbemokun a garin Ipetumodu a jihar Osun, sun roƙi Gwamna Ademola Adeleke da ya cire Sarkin
  • Sun bukaci ya ayyana kujerar Apetumodu ta zama a buɗe bayan hukuncin domin ba da damar neman kujerar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Gidajen Sarauta a jihar Osun sun tura roko ga Gwamna Ademola Adeleke domin ya yi gaggawar tsige Sarki.

Masarautun sun bukaci hakan ne daga Gwamna Adeleke kan Sarkin Ipetumodu bayan Kotun Amurka ta same shi da laifi.

An roki gwamna ya tsige Sarki kan abin kunya
Gwamna Ademola Adeleke da Sarki da aka tura gidan kaso a Amurka, Joseph Oloyede. Hoto: Hon. Jimoh Abayomi.
Source: Facebook

Rahoton The Sun ya ce mutanen sun roƙi Gwamna Ademola Adeleke da ya ayyana kujerar Apetumodu ta zama a buɗe domin samun damar gadonta.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun magantu kan zargin kisan Kiristoci, sun roki Tunibu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin da aka yankewa Sarki a Amurka

An yanke wa Oba Joseph Oloyede hukuncin shekaru hudu da watanni takwas a gidan yari daga kotun tarayya ta Amurka a ranar 26 zuwa 27 ga watan Agusta 2025.

Hakan ya biyo bayan amsa laifinsa kan zambar kuɗaɗen tallafin COVID-19 da suka kai miliyoyin daloli.

Bukatar gidajen sarautan Osun kan Sarki

A wata sanarwa da wakilan gidajen sarautar suka fitar ranar Laraba, sun bukaci gwamnan da ya tabbatar da tsige Sarkin bisa dokar sarauta ta jihar Osun.

Sun tabbatar da cewa an same shi da laifin da ya zubar da mutuncin kujerar sarauta da al’adar gargajiya wanda hakan bakon abu ne a wurinsu tun shekaru da dama da suka wuce.

An bukaci gwamna ya tsige Sarki domin ba da damar neman kujerar
Gwamna Ademola Adeleka na jihar Osun. Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Source: Twitter

An roki gwamnan Osun ya tsige Sarki

Sun kuma nemi gwamna Adeleke da ya ayyana kujerar Apetumodu ta zama a buɗe nan take, tare da sanar da hukumar karamar hukumar Ife ta Arewa da sauran masu sarauta a Ipetumodu domin a bi tsarin sarauta yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda Lawal ya tara malaman Musulunci a Zamfara, ya nemi alfarmarsu

Gidajen sarautar sun roƙi gwamnatin jihar da ta umarci Ma’aikatar Shari’a ta adana hukuncin kotun Amurka cikin kundin Najeriya, domin kammala matakin tsige Sarkin bisa tanadin doka.

A cewarsu:

“Muna shirye mu yi aiki tare da Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi da Sarauta da kuma Ife ta Arewa domin tabbatar da sahihin tsari da zai dawo da mutuncin kujerar da amincewar jama’a.”

Sun koka cewa kujerar Apetumodu ta dade a dakace fiye da shekaru uku saboda rashin dawowar Sarkin wanda ke neman jawo rigima a masarautar.

Punch ta ce gidajen sarautar sun bayyana cewa hakan na kokarin jawo lalacewar al’adu da al’ummar Ipetumodu ke alfahari da su.

Ana neman tsige Sarki a Najeriya

Mun ba ku labari a baya cewa Sarkin Ipetumodu ya fara shiga matsalar da ka iya raba shi da sarauta a jihar Osun bayan hukuncin dauri da kotun Amurka ta yanke masa.

Mai martaba Sarkin zai shafe sama da shekara hudu a gidan yarin Amurka bayan kama shi da laifin cinye kudin tallafin COVID-19.

Wannan hukunci ya sa masu ruwa da tsaki a masarautar da masu zaben Sarki suka fara yunkuri tsige shi da kuma maye gurbinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.