Bayan Shan Suka, Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Sakin Maryam Sanda da Sauran Masu Laifi
- Gwamnatin tarayya ta yi tsokaci kan sakin mutanen da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa
- Ministan shari'a ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala tsarin da zai kai ga sako fursunonin da suka samu afuwar ba
- Lateef Fagbemi ya bada tabbacin cewa ba a saki mutanen da suka samu afuwar daga gidajen gyaran hali ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi magana kan sakin Maryam Sanda da sauran fursunonin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa afuwa.
Gwamnatin ta bayyana cewa ba a saki Maryam Sanda ko wani daga cikin sauran fursunonin da aka sanar za su ci gajiyar afuwar Shugaba Tinubu ba.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban lauyan gwamnati kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi (SAN), ya fitar a ranar Alhamis, 16 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe fiye da mutane 10 a sabon harin da suka kai garuruwan Filato
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An soki gwamnatin Tinubu kan yin afuwa
Wannan karin bayani ya biyo bayan cece-kuce da fushi daga jama’a, bayan da aka bayyana sunayen mutanen da za su ci gajiyar afuwar da shugaban kasan ya yi.
An dai bayyana cewa wasu daga cikin wadanda suka samu afuwar sun hada da wadanda aka yanke musu hukuncin kisa, daurin rai da rai, da kuma laifuffukan da suka shafi fataucin miyagun kwayoyi da kisan kai.
Me gwamnati ta ce kan sakin masu laifi?
A cikin sanarwar, Lateef Fagebemi SAN wanda shi ne shugaban kwamitin da ya ba da shawarar afuwar, ya ce duk wadanda suka samu wannan afuwa har yanzu suna tsare, rahoton jaridar The Punch ya zo da labarin.
“Ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya yana so ya fayyace cewa babu wani fursuna da aka saki daga cikin wadanda aka amince su samu afuwar shugaban kasa a wannan sabon zagaye."
- Lateef Fagbemi

Source: Twitter
Ya kara da cewa aikin na cikin matakin karshe na tantancewa, wanda ya hada da duba sunayen wadanda aka bada shawarar su samu afuwa, domin tabbatar da cewa sun cika dukkan ka’idojin doka da tsari kafin a fitar da takardar sakinsu.
“Mataki na karshe bayan amincewar majalisa koli ta kasa shi ne fitar da takardar aiwatarwa wacce za ta tafi ga shugaban gidajen gyaran hali. Wannan matakin yana ba da damar sake dubawa don tabbatar da sahihanci kafin kammala duk wani aiki."
- Lateef Fagbemi
Ministan ya ce wannan tsarin ba jinkiri ba ne, illa dai bin dokoki da tsare-tsare na tabbatar da gaskiya da adalci.
“Dokar kasa ba ta yarda da gaggawa ba, tana tabbatar da adalci. Da zarar an kammala dukkan binciken doka da tsarin da ya dace, za a sanar da jama’a yadda ya kamata."
- Lateef Fagbemi
An soki afuwar da aka yi wa Maryam Sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa iyalin Bilyaminu Bello sun nuna takaicinsu kan afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda.
Iyalin na marigayi Bilyaminu Bello sun ce yafiyar wani abu ne mai matukar muni da iyalin su ka fuskanta.
Sun bayyana cewa babu wanda ya tuntube su kafin yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka tabbatar ta kashe Bilyaminu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

