'Dan Majalisar Jiha Ya Raba Tallafin Naira Miliyan 250 a Jigawa

'Dan Majalisar Jiha Ya Raba Tallafin Naira Miliyan 250 a Jigawa

  • 'Dan majalisar karamar hukumar Dutse, Tasiu Ishaq Soja, ya raba kayan tallafi na Naira miliyan 250 domin tallafa wa jama’arsa
  • Hon. Tasiu Soja ya bayyana cewa wannan ne karo na hudu da yake rabawa mutanensa kayan tallafi a cikin shekara guda
  • Ya ce yana bin sahun gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa al’umma da kuma shirye-shiryen tazarcen gwamnan a 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.


Jihar Jigawa – 'Dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Dutse a majalisar jihar Jigawa, Hon. Tasiu Ishaq wanda aka fi sani da Soja, ya raba kayan tallafin da kudinsu ya kai Naira miliyan 250.

A wajen rabon kayan, 'dan majalisar ya bayyana cewa wannan ne karo na hudu da yake gudanar da irin wannan tallafi domin rage radadin tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a.

Kara karanta wannan

Farouk Lawan: Tsohon 'dan majalisa ya rabu da Kwankwasiyya bayan barin kurkuku

Tasiu Ishaq Soja, gwamna Namadi
Tasiu Ishaq Soja da gwamnan Jigawa, Umar Namadi yayin kadadmar da raba kayan tallafi. Hoto: Aliyu Ibrahim Dutse
Source: Facebook

A bidiyon da Garba Muhammad ya wallafa a Facebook, Hon. Soja ya ce yana yin hakan ne domin koyi da Gwamna Umar Namadi wanda ke taimakon jama’ar jihar.

Tasiu Soja na koyi da Gwamnan Jigawa

Hon. Tasiu Ishaq Soja ya bayyana cewa duk wani aiki da yake yi a karamar hukumar Dutse yana bin tafarkin Gwamna Umar Namadi ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnan ya zama abin koyi wajen gudanar da mulki nagari da ciyar da kowane yanki na jihar gaba.
Ya kara da cewa:

“Duk abin da nake yi domin jama’a, ina yin ne saboda ina ganin Gwamna Namadi yana yi wa jama’ar Jigawa.”

Dan majalisar ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafawa marasa karfi da kungiyoyi don samar da ayyukan yi ga matasa da mata.

Hon. Tasiu ya raba tallafin N250m a Dutse

A wannan karon, cikin kayan da Hon. Tasiu ya raba akwai kekunan dinki 100, injinan markade 100, injinan taliya 200, injinan faci 100, babura 40 da motoci 17.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya na daukar nauyin Boko Haram? Omokri ya ba sanatan Amurka amsa

Injunan markade da aka raba
Wasu daga cikin injunan markade da Hon. Soja ya raba a Dutse. Hoto: Nazir Aley
Source: Facebook

Ya bayyana cewa ya yi haka ne domin inganta sana'o'i da samar wa matasan Dutse ayyuka da kuma habaka tattalin arzikin jihar baki daya.

Tallafin da 'dan majalisar ya raba a baya

Hon. Soja ya bayyana cewa a baya ya raba kayan tallafin Ramadan na Naira miliyan 30, ya aurar da marayu 30.

Ya kama da cewa a lokacin babbar sallah ya raba raguna 137 da kuma shanu 25 ga kungiyoyi da marasa karfi a karamar hukumar Dutse.

Gwamna Namadi ya yabawa Hon. Soja

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda ya halarci taron rabon tallafin, ya bayyana Hon. Soja a matsayin gwarzo mai kishin al’umma.
Ya ce dan majalisar ya cancanci yabo saboda yadda yake sadaukar da dukiyarsa don amfanin jama’a.
Gwamnan ya kara da cewa kafin wannan taron, sun halarci kaddamar da hanya a yankin Limawa da dan majalisar ke yi, wanda ke nuna jajircewarsa wajen samar da ayyukan raya kasa.

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

Taron ya samu halartar shugaban majalisar jihar Jigawa, wasu manyan jami’an gwamnati, da ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na jihar.

APC ta karbi 'yan PDP, ADC a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa an yi gagarumin taron karbar 'yan jam'iyyun adawa zuwa APC a jihar Jigawa.

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun sun nuna cewa sama da mutum 60,000 ne suka sauya sheka zuwa APC daga PDP da sauran jam'iyyu.

Taron ya samu halartar shugaban APC na kasa, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da wasu manyan 'yan siyasa a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng