Tinubu Ya Alakanta Rashin Tsaro da Masu Satar Ma'adinai, Ya Yi Kira ga Duniya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci shugabannin Afirka su haɗa kai wajen ganin satar ma’adinai ta zama laifi a duniya
- Ya ce satar ma’adinai da fitar da su a ɓoye na barazana ga zaman lafiya, ci gaba da tsaron yankunan nahiyar Afrika
- Tinubu ya ce ya mayar da hankali kan dawo da kadarorin da aka sata da kuma amfani da su wajen tallafa wa ‘yan kasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci shugabannin kasashen Afirka su haɗa kai wajen neman duniya ta amince da satar ma’adinan kasashensu a matsayin babban laifi.
Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a lokacin da ya bude taron shekara-shekara na cibiyar yaki da cin hanci ta kasashen yammacin Afirka (NACIWA) da aka gudanar a Asokoro, Abuja.

Source: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya wakilci shugaban kasar a wajen taron.
Dalilin kiran Tinubu ga kasashen duniya
Tinubu ya ce yana da muhimmanci a dauki wannan matsala a matakin duniya domin baiwa kasashen da abin ya shafa damar daukar matakai masu tsauri kan masu aikata laifin.
Ya ce a Najeriya da wasu kasashen yammacin Afirka, kamar Ghana, Mali da Burkina Faso, ana yawan satar ma’adinai musamman zinare, wanda ke haifar da babbar asara ga tattalin arziki.
Rahotannin hukumar NEITI sun nuna cewa ana fitar da biliyoyin daloli na ma’adinai daga yankin a kowace shekara ta hannun ‘yan kasuwa da ke aikata hakan a ɓoye.
Tasirin satar ma’adinai ga tsaro da tattali
Shugaban ƙasar ya ce kudin da ake samu daga satar ma’adinai na taimakawa wajen yada makamai da ƙarfafa ta’addanci da satar mutane.
Business Day ta rahoto ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu
“Satar albarkatun ƙasa tana ta’azzara rashin tsaro, tana kawo yawaitar makamai da kuma ta’addanci a kasashen yammacin Afirka.”
Tinubu ya kara da cewa lokaci ya yi da duniya za ta fahimci cewa wannan laifi na da illa kamar ta’addanci, domin yana haifar da ruɗani, rashin ci gaba da talauci.
Bukatar haɗin kai tsakanin ƙasashen Afrika
Shugaban ƙasar ya bukaci ƙasashen Afirka su ƙarfafa tsarin yaki da cin hanci da rashawa da kuma musayar bayanan kudi a yankin.
Ya ce:
“Babu wata ƙasa da za ta iya yakar zambar kuɗi ita kaɗai. Dole mu haɗa kai da sauran ƙasashe domin magance wannan matsala.”
Tinubu ya yi kira ga cibiyar NACIWA da ta mayar da hankali wajen nazarin harkokin ma’adinai, tsarin kula da kudi da kuma hanyoyin da ake amfani da su wajen safarar kudin haram.
Kokarin dawo da kadarorin da aka sace
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ɗauki matakai na musamman wajen bin diddigin kadarorin da aka sata da dawo da su cikin ƙasa.
Shugaban ya yabawa hukumar EFCC bisa nasarorin da ta samu wajen dawo da kadarorin da suka kai daruruwan biliyoyin Naira.

Source: Facebook
Ya ce gwamnatinsa ta riga ta zuba N100bn daga cikin kadarorin da aka dawo da su cikin tsarin bayar da rance ga ɗalibai.
IMF ya ce ana sace kudin Najeriya
A wani labari na dabam, mun kawo muku cewa asusun ba da lamuni IMF ya koka kan yadda ake fita da kudi ta haramtacciyar hanya a Najeriya.
Shugabar IMF ta yi magana ne yayin taron kasashe na shekara shekara da ake yi yanzu haka a kasar Amurka.
IMF ya tabbatar da cewa zai taimaka wa kashen duniya domin yaki da badakalar kudi domin inganta tattalin arzikinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

