'Abba Na Aiki,' Manyan Abubuwan Alheri 4 da Suka Samu Jihar Kano a Shekarar 2025
- Jihar Kano ta kara matsayi daga na 35 a 2024 zuwa na hudu a 2025 a jadawalin jagororin sauyin yanayi na kasa da SPPN ta fitar
- Wannan na daga cikin nasarorin da jihar ta samu a fannoni daban-daban, da suka shafi ilimi da tattalin arziki da sauransu a bana
- Legit Hausa ta tattaro muhimman nasarori hudu da Kano ta samu a 2025 karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano — Jihar Kano na ci gaba da samun nasarori masu muhimmanci a fannoni daban-daban, da suka shafi shugabanci, ilimi, muhalli da tattalin arziki.
Masana dai na ganin cewa nasarorin sun kara tabbatar da jajircewar gwamnatin Abba Kabir Yusuf wajen kawo sauyi da cigaba mai dorewa a Kano.

Source: Facebook
Nasarori 4 da Kano ta samu a 2025
Abdullahi I. Ibrahim, daya daga cikin masu tallafawa Gwamna Abba Yusuf ta fuskar sadarwa, ya wallafa nasarori hudu da Kano ta samu a 'yan watannin nan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan nasarori da gwamnatin Kano ta samu da ya shafi jihar kai tsaye su ne:
1. Kano ce ta 2 a jadawalin TII
Jihar Kano ta shiga sahun sabon jadawalin jihohi masu gudanar da aiki cikin gaskiya da aminci a 2025 (TII 2025) wanda cibiyar fito da gaskiya da amincin kudi ta CeFTPI ta fitar.
A wannan jadawalin da aka wallafa a shafin CeFTPI, Kano ta zo ta biyu a fadin kasa, saboda ci gaban da ta samu a fannin fito da gaskiya a ayyukan gwamnati, da bin ka’idojin kashe kudaden jama’a.
Rahoton ya bayyana cewa Kano ta samu wannan matsayi ne saboda shirye-shiryen amfani da fasahar zamani wajen gudanar da mulki, kasafin kudi, da hana cin hanci da rashawa da gwamnatin Yusuf ta aiwatar.
Wannan, a cewar CeFTPI, ya kara aminci da yarda tsakanin gwamnati da jama’a tare da karfafa shigar al’umma cikin harkokin mulki.
2. Kano ce ta 4 a kiyaye muhalli
A wani bangare na muhalli, Kano ta samu ci gaba daga matsayi na 35 a 2024 zuwa na 4 a 2025 a cikin jadawalin jagororin sauyin yanayi na kasa da cibiyar SPPN ta fitar.
Rahoton ya yaba wa jihar bisa manufofinta na dashen bishiyoyi, sarrafa shara, da karfafa amfani da makamashi mai tsafta, kuma wanda za a iya sabuntawa.
3. Kano: #1 a adadin masu cin jarabawar NECO
A fannin ilimi kuwa, Kano ta sake zama jagora a kasa bayan da ta fito ta daya a jarrabawar NECO ta 2025, inda jihar ya fi ko’ina yawan daliban da suka samu nasara a darussa biyar da suka hada da Turanci da Lissafi.
Legit Hausa ta rahoto ma’aikatar ilimi ta jihar ta danganta wannan nasara da ingantaccen tallafi ga malamai, gyaran makarantun gwamnati, da shirin ilimi kyauta.

Source: Facebook
4. Kano ce ta 2 a ci gaban kudin shiga (IGR)
Rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ma ya nuna cewa Kano ta zo ta biyu a jihohi masu ci gaba a fannin harajin cikin gida (IGR) bayan ta kusan ninka kudin da take tarawa cikin shekara guda.
Wannan ci gaba, in ji rahoton, ya samo asali ne daga sabunta tsarin karbar haraji ta yanar gizo da inganta yanayin kasuwanci a Kano da aka samu, inji rahoton Daily Trust.
Masana sun ce wadannan nasarori sun nuna irin dabarun shugabanci na Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya mayar da hankali kan gaskiya, samar da cigaba, da inganta walwalar jama’a.
A zantawarmu da Aliyu Abdullahi Utai daga Kano, ya jinjinawa gwamnatin Abba Yusuf kan sauye-sauyen da ta kawo a fannin ilimi da ya bunkasa fannin a jihar.
Aliyu Utai ya ce Gwamnatin Abba ce kawai ta dukufa ainun wajen ganin yara sun samu ingantaccen ilimi, yana mai cewa:
"Kowane gwamna da inda ya fi mayar da hankali, amma mu za mu ce Abba ya ba da fifiko a ilimi, bunkasa matasa, gina ababen more rayuwa da walwalar ma'aikata.
"To mu ko a iya ilimi an biya mu, domin ko makaho ya laluba ya san an gyara makarantu, an samu sababbin tsare-tsare da suka sanya yaran da ba sa zuwa makaranta a da yanzu suna zuwa.
"Gaskiya mu dai Kano sai san barka."
Abba ya yi magana kan zaben 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan wasu kalamai da ake yadawa game da zabe mai zuwa.
Abba Kabir Yusuf ya ce shekarar 2027 ta Allah ce, kuma ba zai bari barazana ta siyasa ta hana shi ci gaba da ayyukan alheri ba a Kano.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin rabon tallafin N150,000 ga marasa karfi, inda ya zargi wasu da yada jita-jita kan gwamnatinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng



