Tashin Hankali: Gwamna Ya Bayyana Bullar Sabuwa Kungiyar Ta’addanci a Yankinsa
- Gwamnan Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya gargadi jama’a kan bullar wata sabuwar kungiyar ta'addanci
- Gwamna ya nuna damuwa kan kungiyar da ya yi zargin wani ɓangaren Boko Haram ne da suka kwararo yankin
- Ya bayyana cewa ƙungiyar ta na iya ƙara lalata tsaro, musamman ganin yadda ‘yan Lakurawa suka riga suka bazu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa — Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya nuna fargaba kan bullar kungiyar ta'addanci a yankin.
Gwamnan ya gargadi jama’a da hukumomin tsaro kan bayyanar wata sabuwar kungiyar da ya yi zargin na da alaka da Boko Haram.

Source: Facebook
Kungiyar Wulowulo: Gwamna Sule ya gargadi jama'a
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin taron tsaro da shugabannin hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a birnin Lafia, babban birnin jihar, cewar Leardership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Injiniya Sule ya ce kungiyar wani ɓangare na Boko Haram mai suna Wulowulo, wanda ta fara shiga yankin Arewa ta Tsakiya.
Ya bayyana damuwarsa cewa bayyanar wannan ƙungiyar na iya ƙara taɓarɓarewar tsaro a yankin, wanda tuni ke fama da matsalar ƙungiyar Lakurawa, wadda ta bazu daga Jihar Kebbi da Sokoto zuwa Jihar Kwara.
Ya ce:
“Kamar yadda kuka sani, wannan sabuwar ƙungiyar ta Wulowulo, ɓangaren Boko Haram ne, ta fara bayyana a yankin Arewa ta Tsakiya.
“Ƙungiyar Lakurawa yanzu ta zama babbar matsala a Kwara. Da farko suna Yammacin Arewa, amma yanzu sun bazu zuwa Arewa ta Tsakiya."

Source: Twitter
Bukatar Gwamna Sule ga jami'an tsaro
Sule, wanda shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya (NCGF), ya bukaci hukumomin tsaro su dauki mataki cikin gaggawa domin hana wannan masifa shiga Jihar Nasarawa, tare da ƙarin kayan aiki da tallafin tsaro daga gwamnati.
Wannan taro na tsaro ya biyo bayan harin da aka kai kauyen Nindama a ƙaramar hukumar Kokona, inda ‘yan bindiga suka kashe mutane takwas.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yawaitar sace-sacen mutane a wasu yankunan jihar, musamman a ƙananan hukumomin Lafia da Karu, inda ya ce dabarun baya ba su isa dakile hakan ba.
“Daya daga cikin dalilan wannan taro shi ne rahotannin tsaro da ke nuna cewa masu aikata laifuffuka daga wasu sassan ƙasar suna ƙoƙarin shiga yankin Arewa ta Tsakiya. Ya zama dole mu ɗauki mataki kafin abin ya yi muni.
“Sace-sace sun ƙaru sosai musamman a Lafia, kuma yanzu sun fara ƙaruwa a Karu. Wannan yana nuna cewa dole mu fito da sabuwar hanya ta yaki da wannan matsala."
- Gwamna Abdullahi Sule
Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta yi shiru ba, sai ta tabbatar da cewa sababbin barazanar tsaro sun tsaya cak kafin su iya zama barazana ga rayuwar al’ummar Nasarawa da Arewa ta Tsakiya baki ɗaya, cewar Sahara Reporters.
2027: Gwamna Sule ya magantu kan magajinsa
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa zai bayyana wanda yake so ya gaje shi a 2027 a fili.
Gwamnan ya gargadi masu mukaman siyasa a jiharsa da su daina bin ‘yan takara kafin lokacin ya yi.
Ya ce zaɓinsa ba zai dogara da son kai ko karbar kudi ba, sai dai wanda yake da ƙwarewa da hangen nesa wajen ci gaban Nasarawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


