Hon. Farouk Lawan Ya Tabo Batun Rayuwa a Gidan Yari bayan Tinubu Ya Yi Masa Afuwa

Hon. Farouk Lawan Ya Tabo Batun Rayuwa a Gidan Yari bayan Tinubu Ya Yi Masa Afuwa

  • Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi magana kan rayuwar da ya yi a gidan gyaran hali a birnin Abuja
  • Farouk Lawan ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan afuwar da ya yi masa bayan kotu ta same shi da laifi
  • Ya bayyana cewa ya koyi darussa masu muhimmanci dangane da rayuwa a zaman da ya yi a gidan gyaran hali

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi magana kan afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa.

Farouk Lawan ya bayyana afuwar a matsayin wata sabuwar dama ta fara sabon babi a rayuwa, musamman a harkar siyasa.

Farouk Lawan ya godewa Tinubu kan yi masa afuwa
Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan. Hoto: Baffa Karaye
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Farouk Lawan ya bayyana farin cikinsa da godiya bisa wannan afuwa da Bola Tinubu ya yi masa.

Kara karanta wannan

An fara kiran a saki Abba Kyari bayan afuwar da Tinubu ya yi wa mutane 175

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farouk Lawan na cikin mutane 175 da Shugaba Tinubu ya yi wa afuwa a ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025.

Tsohon dan majalisar, wanda ya wakilci mazabar Bagwai/Shanono a jihar Kano, an same shi da laifin cin hanci a shekarar 2012, inda kotun tarayya a ranar 22 ga Yuni, 2021, ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.

Me Farouk Lawan ya ce kan zaman gidan yari?

Ya bayyana zamansa a gidan yari ya koya masa darussa masu muhimmanci game da rayuwa da kaddara.

“Idan mutum ya tsinci kansa cikin jarabawa sannan Allah Ya ba shi damar samun afuwa, wajibi ne ya gode. Iyalaina da abokaina daga sassa daban-daban na duniya sun cika da murna da farin ciki da jin wannan labari."
“Ranar da aka yi mini afuwa ranar godiya ce ga Allah, domin shi ne Ya ba da damar haka, sannan ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya yi abin kirki kuma abin yabo.”

Kara karanta wannan

Batanci: Sheikh Lawal Triumph ya fitar da bayanai bayan zama da shura a Kano

- Farouk Lawan

Da yake tunawa da lokacin da ya shafe a gidan yari, Farouk Lawan ya ce ya karɓi kaddararsa da natsuwa tun kafin a tura shi gidan yari, yana mai cewa duk inda mutum ya samu kansa, zai iya rayuwa idan Allah Ya so.

“Kafin ma na isa gidan yari, na riga na yarda da kaddara. Na san zan hadu da mutane, kuma idan wasu sun rayu a can, to ni ma zan iya rayuwa."

- Farouk Lawan

Farouk Lawan ya fice daga Kwankwasiyya

Bayan an sako shi a shekara ta 2024, tsohon dan majalisar ya ce ya dauki matakai na sake daidaita tafiyarsa ta siyasa, inda ya fita daga tafiyar Kwankwasiyya wadda yake da alaka da ita a baya.

Farouk Lawan ya godewa Shugaba Tinubu
Farouk Lawan wanda Tinubu ya yi wa afuwa. Hoto: Farouk M. Lawan
Source: Facebook

Ya bayyana cewa ko da yake yana cikin jam’iyyar PDP lokacin da aka daure shi, daga baya ya umarci magoya bayansa da su shiga NNPP kafin zaben 2023, kuma sun bi wannan umarni.

Kara karanta wannan

'Yan uwan Bilyaminu sun shiga kunci, sun yi tir da Tinubu ya yafe wa Maryam Sanda

Sai dai ya bayyana cewa duk da kusancinsa da tafiyar Kwankwasiyya, wani babban jigo a cikin tafiyar bai taba kiransa ba don taya shi murna ko nuna juyayi tun bayan fitarsa daga gidan yari ba.

Duk da haka, Lawan ya bayyana cewa yana mutunta jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da cewa yanzu ba ya cikin tafiyar siyasarsu.

A lokacin da yake tsare, Legit Hausa tana da labari cewa an rika ganin tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso ya kai masa ziyara a gidan maza.

An bukaci Tinubu ya yi wa Abba Kyari afuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya bukaci a yi wa DCP Abba Kyari afuwa.

Solomon Dalung ya nuna cewa bai kamata a ci gaba da shari'ar da ake yi wa dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sandan ba.

Tsohon ministan ya bayyana cewa Abba Kyari ya cancanci a yi masa afuwa, muddin har za a iya yi wa masu garkuwa da mutane, safarar kwayoyi da ya taba cafkewa a baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng