An Fara Kiran a Saki Abba Kyari bayan Afuwar da Tinubu Ya Yi Wa Mutane 175
- Ana ci gaba da tafka muhawara kan afuwar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa wasu 'yan Najeriya
- Tsohon ministan wasanni da matasa ya yi kiran da a yi irin wannan afuwar ga DCP Abba Kyari wanda ake shari'arsa a kotu
- Solomon Dalung ya nuna cewa bai kamata a ci gaba da tsare DCP Abba Kyari duba da irin rawar da ya taka wajen kama masu laifi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar Movement for the Emancipation of Nigeria (MEN) karkashin jagorancin Solomon Dalung, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shari’ar da ake yi wa, DCP Abba Kyari.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta sakin DCP Abba Kyari wanda aka dakatar.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung, ya fitar a shafin Facebook a ranar Talata, 13 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan
Hon. Farouk Lawan ya tabo batun rayuwa a gidan yari bayan Tinubu ya yi masa afuwa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya yi afuwa ga masu laifi
A watan Maris na shekarar 2022, hukumar NDLEA ta gurfanar da Kyari tare da wasu mutum shida bisa zargin hada baki wajen amsar wani abu daga kwayoyi masu nauyin kilogiram 21.35 da aka kwace daga wasu masu safarar miyagun kwayoyi.
A makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu ya yi wa mutane 175 afuwa, ciki har da marigayi Herbert Macaulay, marigayi Manjo Janar Mamman Vatsa, da Maryam Sanda, wacce aka yanke wa hukuncin kisa kan laifin kashe mijinta.
An koka kan ci gaba da tsare Abba Kyari
Kungiyar ta ce ci gaba da tsare Abba Kyari babban zalunci ne, ganin yadda Shugaba Tinubu ya yi wa wasu fursunoni afuwa, ciki har da wadanda Kyari da tawagarsa suka kama a baya.
“Kungiyar MEN ta lura cike da damuwa yadda ake ci gaba da tsare DCP Abba Kyari duk da afuwar da aka yi wa masu laifi kamar masu safarar miyagun kwayoyi, masu damfara, masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi, wadanda da yawansu tawagarsa ce ta kama yayin da suke gudanar da aikinsu."
- Solomon Dalung
Kungiyar MEN ta bayyana irin wannan fifiko a aikace a matsayin take adalci da nuna son kai, tana mai cewa hakan ya rushe hujjar ci gaba da tsare Kyari.
“Sabuwar afuwar da aka yi ta rushe hujjar ci gaba da tsare DCP Kyari. Ci gaba da shari’arsa karkashin irin wannan yanayi yana nuna wariya wadda ta rage darajar tsarin shari’a a Najeriya."
- Solomon Dalung
An soki ci gaba da shari'ar Abba Kyari
Kungiyar ta yi gargadin cewa ci gaba da shari’ar na iya zama mummunan misali da zai rage kwarin gwiwar jami’an tsaro wajen yaki da laifuffuka.

Source: Getty Images
"MEN ta dauki hakan a matsayin cin amanar ma’aikacin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare tsaro da doka."
"Adalci yana bukatar daidaito, kuma tausayi bai kamata ya zama na masu laifi kawai ba, yayin da ake hukunta masu gaskiya."
- Solomon Dalung
A karshe, kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da babban lauyan gwamnatin tarayya su dakatar da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi wa DCP Abba Kyari tare da ba da umarnin sakinsa nan take.

Kara karanta wannan
An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu
Dalilan rage zaman gidan yari ga fursunoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rage wa'adin zaman gidan yarin da wasu mutane za su yi.
Mutanen da aka rage shekarun da suka kwashe a gidan gyaran hali na daga cikin wadanda Shugaba Tinubu ya yi wa afuwa.
An bayyana cewa an rage musu wa'adin saboda nuna nadama, koyon sana'a a zaman da suke yi a gidan gyaran hali.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
