Afuwar Tinubu: Dalilan Tinubu na Ragewa Mutane 18 Zaman Gidan Yari

Afuwar Tinubu: Dalilan Tinubu na Ragewa Mutane 18 Zaman Gidan Yari

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi afuwa ga wasu 'yan Najeriya da aka yankewa hukunci.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Shugaba Bola Tinubu ya yi afuwar ne ga mutane 175, kan laifuffuka daban-daban da aka same su da su.

Shugaba Tinubu ya yi wa wasu 'yan Najeriya afuwa
Mai girma Shugaba Bola Tinubu a ofis. Hoto: @DOlusegu
Source: Facebook

Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Tinubu ya yi sassauci kan zaman gidan yari

Daga cikin mutanen da aka yi wa afuwar, akwai wadanda aka yi musu sassauci kan zaman da suke yi a gidan yari.

A jimilla, an ragewa mutane 65 yawan shekarun da za su kwashe a gidajen gyaran hali.

An bada dalilin yin sassauci ga mutane 18 daga cikinsu, yayin da sauran kuma ba a bayyana ba.

Wasu daga cikinsu an yi musu sassaucin ne saboda nuna kyakkyawan hali a zaman da suke yi a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Kasurgumin mai garkuwa da mutane, Ezigbe ya ci moriyar afuwar Shugaba Tinubu

Ga waau daga cikin wadanda aka yi wa sassauci da dalilin rage musu zaman gidan yari.

1. Yusuf Owolabi (mai shekara 36)

An yanke masa dauri na rai da rai a shekarar 2015 saboda kisan kai. Ya shafe shekaru 10 a gidan yarin Kirikiri.

An rage masa hukuncinsa zuwa shekaru 12 saboda nuna nadama da koyon sana’ar hannu a gidan yari.

2. Ifeanyi Eze (mai shekara 33)

An yanke masa dauri na rai da rai a shekarar 2021 saboda kisan kai. Ya shafe shekaru hudu a gidan yarin Kirikiri.

Hukuncinsa ya ragu zuwa shekaru 12 a tsae saboda nadama da koyon sana’ar hannu da ya yi yayin da yake garkame.

3. Malam Ibrahim Sulaiman (mai shekara 59)

An yanke masa dauri na rai da rai a 2022 saboda fashi da makami da mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta ce hukuncinsa ya ragu zuwa shekaru 10 saboda nuna kyakkyawan hali.

4. Shettima Maaji Arfo (mai shekara 54)

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya fadi dalilin jifar Najeriya da zargin ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi

An yanke masa shekaru bakwai a 2021 saboda cin hanci da rashawa wanda laifi ne a karkashin dokokin Najeriya.

Hukuncin ya ragu zuwa shekaru hudu saboda kyakkyawan hali da kuma rashin lafiya ta ke fama da shi a gidan maza.

5. Ajasper Benzeger (mai shekara 69)

An yanke masa shekaru 20 a shekarar 2015 saboda kisan kai. Zuwa yanzu ya shafe shekaru 10 yana tsare a kurkuku.

Hukuncinsa ya ragu zuwa shekaru 12 saboda tsufarsa da rashin lafiya. An ragewa tsohon mai kusan shekaru 70 a duniya zaman kaso.

6. Ifenna Kennechukwu (mai shekara 42)

An yanke masa shekaru 20 a 2015 saboda shigo da kwayoyi (hodar iblis). Ya shafe kusan shekaru 10 a Kirikiri.

Shi ma dai kamar yadda sanarwa ta gabata, hukuncinsa ya ragu zuwa shekaru 12 saboda nadama da koyon sana’ar hannu.

7. Mgbeike Matthew (mai shekara 45)

An yankewa Mgbeike Matthew hukuncin daurin shekaru 20 a shekarar 2013 saboda shigo da kilo 3.10 na kwaya.

Saboda nuna nadama da koyon sana’ar hannu a Kirikiri, an rage hukuncinsa zuwa shekaru 12, yana cikin wadanda aka yi wa rangwamen shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Maryam Sanda ta shiga jerin wadanda aka yafewa, Tinubu ya fadi dalilin yafe mata

8. Odeyemi Omolaram (mai shekara 65)

An yanke masa daurin shekaru 25 a 2017 saboda laifin safarar kwayoyi. Yana cikin mutanen da shugaban kasa ya tausaya masu.

Hukuncinsa ya ragu zuwa shekaru 12 saboda nadama da tsufarsa. Tuni dai kungiyoyi irinsu HURIWA suka yi tir da wannan afuwa.

9. Ada Audu (mai shekara 72)

An yanke mata shekaru bakwai a shekarar 2022 a Gidan Yarin Kuje, inda ta shafe shekaru biyu da watanni bakwai.

Hukuncin ya ragu zuwa shekaru hudu saboda tsufarta. Tana cikin matan da shugaba Bola Tinubu ya yi wa afuwa a bana.

10. Kelvin Oniarah Ezigbe (mai shekara 44)

An yanke masa shekaru 20 a watan Oktoba 2023 saboda yin garkuwa da mutane, wanda hukuncin ya fara aiki tun 2013.

Hukuncin Kelvin Oniarah Ezigbe ya ragu zuwa shekaru 13 saboda nadama da halartar jami’ar National Open University (NOUN)

11. Frank Azuekor (mai shekara 42)

An yanke masa shekaru 20 a 2023 saboda yin garkuwa da mutane, kuma ya shafe shekaru 12 tun 2013 a Kuje.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa da laifin da suka aikata

Hukuncinsa ya ragu zuwa shekaru 13 saboda kyakkyawan hali da halartar jami'ar National Open University (NOU).

12. Iyabo Binyoyo (mai shekara 49)

An yanke mata shekaru 10 a 2017 saboda laifin safarar kwayoyi. Masu irin laifinta su ne kusan 30% na wadanda aka yi wa afuwa.

Hukuncinta ya ragu zuwa shekaru tara saboda nuna kyakkyawan hali da ta yi yayin da ta samu kan ta a gidan kurkukun.

13. Oladele Felix (mai shekara 49)

An yanke masa shekaru biyar a 2022 saboda laifin hada baki wajen yin cin zali, ba tare da zaɓin tara ba.

Hukuncin zaman gidan yarin da yake yi a Suleja ya ragu zuwa shekaru hudu saboda kyakkyawan hali da nadama.

14. Rakiya Beida (mai shekara 33)

An yankewa Rakiya Beida hukuncin shekaru bakwai a 2021 saboda sata da zamba, ba tare da zaɓin tara ba.

Hukuncin zaman gidan yarin da take yi a Suleja ya ragu zuwa shekaru uku saboda kyakkyawan hali.

Shugaba Tinubu ya yi sassauci ga wasu 'yan Najeriya
Shugaban kasa Bola Ahmed Bola Tinubu. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

15. Manjo S.A. Akubo (mai shekara 62)

An yanke masa daurin rai da rai a 2009 a gidan yarin Katsina saboda satar makamai 7,000, ya saidawa tsagerun yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane yayin da 'yan sanda suka kashe miyagu a Zamfara

Kamar sauran wadanda aka yi wa sassauci, hukuncinsa ya ragu zuwa shekaru 20 saboda nuna kyakkyawan hali da nadama.

16. John Ibiam (mai shekara 39)

An yanke masa shekaru 15 a 2016 saboda kisan kai, ya shafe shekaru tara da wata daya a gidan yarin Afikpo.

Hukuncinsa ya ragu zuwa shekaru 10 saboda nuna nadama da koyon sana’ar hannu a gidan yari.

17. Umanah Ekaette Umanah (mai shekara 70)

An yankewa Umanah Ekaete Umana shekaru 10 a 2022 a Port Harcourt saboda yin amfani da takardun bogi.

Hukuncinta ya ragu zuwa shekaru biyar saboda tsufarta da yin nadamar laifin da aikata yayin zamanta a gidan gyaran hali.

18. Utom Obong Thomson Udoaka (mai shekara 60)

An yanke masa shekaru bakwai a 2020 a Ikot Ekpene saboda zamba da karɓar kuɗi ta hanyar yaudara. Ya shafe shekaru hudu da watanni biyu a kurkuku.

Hukuncin ya ragu zuwa shekaru biyar saboda tsufarsa da nuna kyakkyawan hali yayin zamansa a gidan yari.

ADC ta soki Tinubu kan yin afuwa

Kara karanta wannan

Sallama da murabus: Jerin ministoci 9 da aka rasa a gwamnatin Bola Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ta soki matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na yi wa wasu 'yan Najeriya afuwa.

ADC ta bayyana matakin Shugaba Tinubu a matsayin abin takaici, kuma abin kunya ga kasa baki daya.

Jam'iyyar ta ce Tinubu na yafewa wadanda aka kama da laifuffukan da su ka shafi safarar miyagun kwayoyi babbar nakasu ce ga kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng