Gwamnan Plateau Ya Gwangwaje Wata Hajiya bayan Ta Tsinci Kudi a Saudiyya

Gwamnan Plateau Ya Gwangwaje Wata Hajiya bayan Ta Tsinci Kudi a Saudiyya

  • Wata Hajiya daga jihar Plateau ta nuna halin kwarai yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025 a kasa mai tsarki watau Saudiyya
  • Hajiyar mai suna Zainab Idris ta mayar da wasu kudaden da ta tsinta na wani Alhaji wanda ya fito daga kasar Tajikistan
  • Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang ya yaba da halin kirkin da ta nuna, inda ya gwangwaje ta da kyautar kudi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya bai wa wata Hajiya mai suna Zainab Idris kyautar Naira miliyan ɗaya (N1,000,000).

Gwamna Mutfwang ya ba ta kyautar ne saboda mayar da kuɗi Dala $5,000 da ta tsinta na wani Alhaji dan kasar Tajikistan.

Gwamna Mutfwang ya ba wata Hajiya kyauta
Gwamna Caleb Mutfwang a wajen wani taro. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce an mika mata kyautar ne a ofishin hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Plateau, ta hannun sakataren sukumar, Alhaji Dayyabu Dauda.

Kara karanta wannan

An fara guna guni da Majalisar Benue ta amince gwamna ya karbo bashin Naira biliyan 100

Hajiya daga Plateau ta tsinci kudi a Saudiyya

Zainab Idris, wadda ta fito daga jihar Plateau, ta tsinci kuɗin ne a kasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.

Bayan ta tsinci kudin, ta nemi mai su sannan ta damka masa kudadensa.

Wace kyauta Gwamna Mutfwang ya ba ta?

Sakataren hukumar jin dadin Alhazan ya ce Gwamna Mutfwang ya umurci a gayyace ta don nuna godiya da yabo ga kyawawan halayenta, tare da taimaka mata da ɗan karamin jari don ci gaban kasuwancinta.

Hakazalika, gwamnan ya bai wa wani Alhaji, Malam Ayuku, sabuwar wayar hannu saboda mayar da wata wayar iPhone da ya tsinta yayin aikin Hajji a Saudiyya.

Da yake jawabi, Alhaji Dayyabu Dauda ya ce:

“Muna alfahari da waɗannan Alhazai saboda sun nuna halin kirki da gaskiya. Kafin tafiyarmu kasar Saudiyya, gwamna ya yi kira gare su da su zama jakadu na gari, kuma sun tabbatar da hakan da aikinsu. Lallai muna alfahari da su."

Kara karanta wannan

Majalisa ta cin ma matsaya kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya

Ya kara da cewa Gwamna Mutfwang ya yi kira sauran mutanen jihar da ma Najeriya gaba ɗaya da su yi koyi da irin wadannan halayen na gaskiya da amana.

“Gwamna Mutfwang ya bada shawarar cewa mu zama masu hali nagari a duk inda muka tsinci kanmu. Ya kuma yi kira ga sauran mutanen jihar da 'yan Najeriya kan mu yi koyi da su."

- Alhaji Dayyabu Dauda

Gwamna Mutfwang ya ba wata Hajiya kyautar kudi
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

A nata jawabin, Zainab Idris ta nuna godiyarta ga gwamnan, tana mai cewa kyautar za ta taimaka mata sosai wajen faɗaɗa kasuwancinta, tare da yabawa gwamnan bisa kulawarsa ga al’umma.

EFCC ta gayyaci shugaban NAHCON

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gayyaci shugaban hukumar Alhazai ta kasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman.

Hukumar EFCC ta gayyace shi ne bisa zargin karkatar da kudi da suka kai sama da Naira biliyan 50 da suka shafi shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2025.

Binciken da EFCC ke gudanarwa na da nufin gano gaskiya kan zargin da ya shafi karkatar da makudan kudi da suka kai fiye da Naira biliyan 50 daga asusun hukumar NAHCON.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng