Ta Faru Ta Kare, ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki a dukkanin Jami'o'in Najeriya

Ta Faru Ta Kare, ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki a dukkanin Jami'o'in Najeriya

  • Kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta gaji da gafara sa ba ta ga kaho a alkawuran da gwamantin tarayya ke yi mata.
  • ASUU ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu a duk jami’o’in gwamnati da ke Najeriya daga Litinin, 13 ga Oktoba, 2025
  • Farfesa Chris Piwuna, ya ce babu wani abin da zai hana aiwatar da wannan yajin aikin bayan cikar wa’adin kwanaki 14
  • Sanusi Ya'u Mani, wakilin daliban Hakimin Mani , ya shaidawa Legit Hausa cewa akwai bukatar a samar da mafita ta dindindin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, wato ASUU, ta ayyana shiga yajin aiki na gargaɗi mai tsawon makonni biyu.

Kungiyar ASUU ta tabbatar da shiga yajin aikin ne a duk jami’o’in gwamnati a fadin ƙasar bayan rashin daidaito da gwamnati.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Kungiyar ASUU ta fara yajin aiki a Najeriya
Shugaban kungiyar ASUU da ministan ilimi a Najeriya. Hoto: Federal Ministry of Education.
Source: Twitter

Kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki a Najeriya

Shugaban kungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da Punch ta bibiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Piwuna ya tabbatar da shirin shiga yajin aikin a yau Lahadi 12 ga watan Oktoban 2025 inda ya ce babu abin da zai hana su tafiya.

Farfesa Piwuna ya ce:

“Babu wani abu da ya isa ya hana aiwatar da shawarar da majalisar ASUU ta yanke na shiga yajin aiki bayan cikar kwanaki 14 da muka sanar tun 28 ga Satumba.”

Ya ƙara da cewa dukkan rassan ASUU a jami’o’i za su dakatar da ayyukansu daga karfe 12 na dare ranar Litinin, 13 ga Oktoba, 2025.

Ya bayyana cewa yajin aikin zai kasance “cikakke kuma gaba ɗaya” kamar yadda aka amince a taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC).

Wannan mataki, a cewarsa, ya zama dole saboda gwamnati ta kasa aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a baya.

Kara karanta wannan

Amupitan: Jam'iyyar ADC ta aika sako ga sabon shugaban INEC da Tinubu ya nada

Gwamantin Tinubu ya magantu kan yajin aikin ASUU
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Majalisar Dinkin Duniya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Abin da gwamnatin Tinubu ta ce kan ASUU

Sai dai a bangaren gwamnati, Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ce gwamnati tana kokari wajen tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi domin warware matsalolin albashi, tallafi, da aiwatar da yarjejeniyar 2009.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta riga ta saki Naira biliyan 50 domin biyan kudaden alawus alawus.

Har ila yau, ta yi magana kan ƙarin Naira biliyan 150 da aka saka a cikin kasafin kudin 2025 don bukatun gyaran jami’o’i, cewar Leadership.

Sai dai kungiyar ASUU ta ce wadannan alkawura ba su wadatar ba domin tabbatar da dawwamar daidaito da walwala a jami’o’in gwamnati, don haka ta fara yajin aikin.

Ya kamata a samar da mafita ta dindindin

A zantawar Legit Hausa da Sanusi Ya'u Mani, wakilin daliban Hakimin Mani a jihar Katsina, ya ce akwai bukatar a samar da mafita ta dindindin.

Kara karanta wannan

Durkusa wa wada: Gwamnatin Tinubu ta roki ASUU, ta dauki sabon alkawarin hana yajin aiki

Sanusi Ya'u Mani ya ce:

"Ba na tunanin wannan yajin aikin na gargadi an shige shi don cutar da tsarin karatu, ya fi kama da tunatarwa ga gwamnati kan cika alkawuran da ta dauka tun da dadewa.
"Ya kamata gwamnati ta gane cewa jinkiri wajen biyan hakkokin malamai da inganta jami’o’i yana rage musu kwarin gwiwa, kuma yana lalata ingancin karatu.
"Ita kuma ASUU ta gane cewa abin da hakuri bai bayar ba, rashin hakuri ba zai samar da shi ba, kawai ta ci gaba da tattaunawa da gwamnati domin kada dalibai su sake zama wadanda rikicin zai fi shafa."

Sanusi Ya'u ya ce abin da ake nema a yanzu shi ne mafita mai dorewa, saboda yajin aiki kadai ba zai magance matsalolin jami'o'i gaba daya ba.

"Ina rokon gwamnati da ASUU su zauna teburin tattaunawa cikin gaggawa, domin ceton tsarin ilimi da makomar matasan Najeriya."

- Sanusi Ya'u Mani.

Yajin aiki: Gwamnati ta roki kungiyar ASUU

Kara karanta wannan

UNICEF: Yadda Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 10 a Bauchi da jihohin Arewa 5

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin tarayya ta roƙi kungiyar malaman jami'o'i ta kasa, ASUU da ta dakatar da yajin aikin da ta ke shirin fara wa a Najeriya.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya taushi kungiyar malaman, inda ya ce ana ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin ASUU.

ASUU ta ba gwamnati wa’adin kwana 14, kuma idan ba a biya buƙatunta ba, za a fara yajin aiki na gargadi kafin a dauki mataki na gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com