'Yan Bindiga Sun Farmaki Bayin Allah a Nasarawa, an Samu Asarar Rayuka
- An shiga jimami bayan wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Miyagun 'yan bindigan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ciki har da wadanda aka yanka
- Lamarin ya auku ne bayan da 'yan bindigan suka yi dirar mikiya kan mutanen wani kauye a karamar hukumar Kokona
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - 'Yan bindiga sun hallaka akalla mutane tara ciki har da takwas da aka yanka, a jihar Nasarawa.
'Yan bindigan sun kai mummunan harin ne a kauyen Nindama da ke karamar hukumar Kokona ta jihar Nasarawa.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne cikin tsari a safiyar Juma’a, 10 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun yi barna a Nasarawa
'Yan bindigan sun shiga kauyen ne suna harbi kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutane da dama.
Wasu mutane shida kuma ba a san inda suke ba sakamakon harin na 'yan bindiga.
Wani ganau da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa mutane biyu sun sami mummunan rauni, kuma an garzaya da su zuwa asibiti, yayin da jami’an tsaro suka fara kokarin ceto mutanen da aka sace da kuma bin diddigin maharan.
Rahotanni sun kuma ce da misalin ƙarfe 3:30 na rana a ranar Asabar, tawagar sojoji, ‘yan sanda, jami’an DSS, NSCDC da ‘yan sa-kai tare da shugaban karamar hukumar Kokona, Hon. Agbawu M. Agbawu, sun ziyarci inda lamarin ya auku.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kai gawarwakin mutanen da aka kashe zuwa dakin ajiye gawa, kuma binciken farko ya nuna cewa harin na iya zama mai nasaba da rikicin filaye da ya daɗe a yankin.
Kungiyar matasan Tiv ta la’anci kisan matashiya
A wani lamari daban, kungiyar matasan Tiv (TYO) ta la’anci kisan gilla da aka yi wa Favour Akaaza ‘yar ƙauyen Imon, da ke masarautar Adudu a karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.

Source: Original
An ruwaito cewa maharan sun sace ta daga gidanta da ke yankin Ombi Anzaku a kan hanyar Kwandere, sannan daga bisani suka kashe ta.
Kungiyar TYO reshen jihar Nasarawa ta bayyana cewa mutanen da suka aikata wannan aika-aika Fulani ne da aka riga aka kama kuma sun amsa laifin.
“Muna kallon wannan aiki a matsayin ta’addanci, rashin imani, da hari kai tsaye ga zaman lafiya da tsaron al’umma."
"Abin takaici ne cewa irin wannan matashiya mai tasowa ta rasa rayuwarta a hannun waɗanda ba su da imani ko sanin darajar ran ɗan Adam.
- Kungiyar TYO
'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun yi ta'asa kan jami'an tsaro na CJTF a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun hallaka jami'an tsaron har guda takwas bayan sun yi musu kwaton bauna a karamar Tsafe.
Lamarin ya auku ne lokacin da jami'an tsaron ke shirin kai daukin gaggawa bayan samun shirin 'yan bindiga na kawo hari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


